An gano cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya raba wa sanatoci kowane naira milyan biyu a matsayin kuɗin tafiya gida a ji daɗin hutun makonni bakwai da su ka tafi.
Wani sanata da ya nemi a sakaya sunan sa, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa dukkan sanatocin 109 an bai wa kowa kuɗin tafiya hutun, wanda za su fara a ranar Litinin, su koma Majalisa ranar 26 Ga Satumba.
Lissafi ya nuna cewa, idan kowane daga cikin su ya karɓi naira miliyan 2, to an yi masu watandar Naira miliyan 218 kenan.
Kowanen su dai ya ji saukar ‘alert’ a cikin asusun ajiyar bankin su a ranar 8 Ga Yuli, kafin Akpabio ya yi suɓul-da-bakan sanar da su kuɗaɗen a fili.
Sai dai kuma ba a tantance ko nawa aka tura wa masu riƙe da muƙamai a Majalisar Dattawa ba, waɗanda na su kason sai fi yawan na sauran sanatoci.
Naira miliyan 2 da aka bai wa kowane sanata dai haramtattu ne, domin babu su a tsarin kuɗaɗen da doka ta amince a bai wa sanatocin.
Akpabio dai ya janyo ce-ce-ku-ce, yayin da ya yi wa sanatoci watandar kuɗaɗe duniya na kallo.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya janyo wa kan sa ce-ce-ku-ce da ragargaza a faɗin ƙasar nan, yayin da ya bayyana wa sanatoci cewa, “kowa ya saurari saƙon ‘alat’ na saukar hasafin kuɗaɗin more zaman gida da ku yi a lokacin hutun majalisa.”
Akpabio ya manta cewa a zauren Majalisar Dattawa ya ke, kuma ga kyamarori na haska shi duniya na kallo kai-tsaye.
Tuni magulmata su ka gutsiri bidiyon aka watsa da soshiyal midiya, lamarin da ya janyo ake ci gaba da ragargazar Akpabio da Sanatoci baki ɗaya.
An fallasa guntun bidiyon a ranar Laraba, amma dai tun a ranar Litinin ce Akpabio ya yi suɓul-da-baka ɗin, bayan sun kammala tantance ministocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sanatoci dai sun tafi hutu, sai ranar 26 Ga Satumba za su koma majalisa.
“An tura wa kowa wani hasafin da zai riƙa kashewa ya na ɓalle-bushasha a lokacin hutun da za mu tafi.”
Zarar Bunu: Yadda Akpabio Ya Yi Ƙoƙarin Waskewa:
Bayan ya yi kasassaɓar da ya tafka, wasu sanatoci sun yi gaggawar nusar da shi katoɓarar da ya yi, inda shi kuma nan da nan ya waske kamar haka:
“To na janye maganar da na yi”, sannan kuma ya ƙara da cewa:
“Majalisar Dattawa ta aika wa kowanen ku da saƙon kyakkyawar addu’a, fatan za ku ji daɗin hutun da za mu tafi.”
Ba a dai san adadin da aka tura wa kowane sanata domin ya tafi gida ya ɓalle bushasha ba.
Amma dai wasu na ganin cewa watakila kuɗin hutu Akpabio ya so ya ce, ba hasafin ɓalle-bushasha a lokacin hutun ba.
Discussion about this post