Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa wasu ‘yan kacakaura ne da ‘yan ƙaƙuduba su ka dakatar da ɗan takarar shugaban ƙasa, Sanata Rabi’u Kwankwaso, amma ba NNPP ba ce.
NNPP ta ce waɗanda su ka dakatar Kwankwaso korarrun ‘yan jam’iyya ne, waɗanda aka dakatar tsawon watanni uku, daga baya kuma aka kore su daga jam’iyyar kwata-kwata.
Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Kwamitin Zartaswar NNPP na Ƙasa, a wani taron manema labarai da jam’iyyar ta gudanar ranar Laraba, a Abuja.
Ladipo Johnson, Babban Mai Binciken Kuɗin NNPP na Ƙasa ne ya yi wa manema labarai jawabi a lokacin ganawa da manema labarai a Hedikwatar NNPP.
Johnson, wanda shi ne tsohon Kakakin Yaɗa Labaran Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Kwankwaso, ya ce dakatarwar da wasu ‘yan ƙaƙuduba su ka yi wa Kwankwaso shirme ce, kuma sakarci ne kawai.
A ranar Talata ce dai aka tashi da labarin dakatar da Kwankwaso daga NNPP, wanda wani ɓangare na jam’iyyar bisa jagorancin tsohon Shugaban Kwamitin Dattawa, Boniface Aniebonan ya yi sanarwa.
Sanarwar ta su ta ce sun dakatar da Kwankwaso tsawon watanni shida daga NNPP, saboda zargin ya na aikata ayyukan da suka saɓa wa NNPP.
Ɓangaren su Boniface sun yi taron su daban ne a Legas.
Sannan kuma su ka naɗa Majo Agbo a matsayin Shugaban Riƙon NNPP.
Sai dai kuma Johnson ya shaida wa manema labarai cewa da Boniface da Agbo duk korarru ne daga NNPP.
Ya ce a taron Shugabannin NNPP da aka gudanar a Abuja ranar Talata, wanda kuma INEC ta aika da wakilin ta ya sa-ido, an naɗa sabbin shugabanni, an canja tambarin jam’iyya kuma an jaddada korar Boniface da Agbo.
“Saboda haka abin dariya ne a ce waɗanda jam’iyya ta dakatar, sannan ta kore su, a ce kuma su ne daga baya za su ce sun dakatar da Kwankwaso kuma wai sun rushe shugabannin NNPP.” Inji Johnson.
Discussion about this post