Ƴan bindiga sun kashe wani malamin Arabi Malam Murtala sannan sun yi garkuwa da wasu mutum bakwai a garin Bungudu dake jihar Zamfara ranar Litinin.
Bungudu na daga cikin garuruwan dake fama da hare-haren ƴan bindiga a Zamfara.
Majiya daga garin Ibrahim Bungudu ya ce maharan sun yi garkuwa da Abdurrahman Hassan babban dan sarkin Bungudu, Abubakar Sarkin-Fada tsohon ma’aikacin gwamnati, Amina Salisu wata matar aure sannan da wasu mata hudu.
Bungudu ya ce kai tsaye maharan suka shiga gidajen mutane suna tafiya da su ba tare da wani shamaki ba.
Babangida Sarkin fada ya ce a cikin gidansu maharan suka shigo suka tafi da mahaifinsa Sarkin fada, shi kadai.
Haka kuma wani mazaunin kauyen Zaharadeen Sani na zargin cewa akwai hannun masu hada baki da mahara a wannan harin.
Zuwa yanzu dai mazauna garin sun ce maharan ba su kira neman kudin fansa ba.
Bayan haka dan majalisar wakilai ta kasa dake wakiltan Maru/Bungudu Abdulmalik Zubairu ya koka da rashin tsaron da ake fama da shi a garin Bungudu yayin ya yi kira ga gwamnatin tarayya da jihar da su dauki tsauraran matakan da za su taimaka wajen samar da tsaro a yankin.
Idan ba a manta ba a makon jiya ƴan bindiga sun kashe wani dan sanda Nura Ibrahim a hari da suka kai ofishin ƴan sanda na Bungudu.
Discussion about this post