Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi, ya fusata a lokacin da yake bibiyar yadda aka rabawa manoma tallafin korana a karamar Hukumar Rimgin a ranar Lahadi.
Gwamna Namadi ya yi ziyarar ne domin ya gano yadda talakawa manoma suka amfana ko akasin haka da kudin tallafin Korona da Bankin Duniya (World Bank) ta baiwa Jihar ta Jigawa kyauta domin rage raɗaɗin talauci samakon kullen Korana data jefa mutanen Jihar.
Manoma a fadin Jihar ta Jigawa sun amfana da kyautar taki da maganin feshi daga tallafin na Bankin Duniya wanda gwamnan ya ke zargin baiwa jihar ga manoman ba kamar yadda aka tsara.
Yace duk wanda ya ci kudin sai ya biya kamar ya faɗi.
Discussion about this post