Majalisar Wakilai ta amince da Naira Biliyan 500 da Shugaba Bola Tinubu ya nema na samar da kayan agajin gaggawa domin rage radadin cire tallafin man fetur ga ‘yan Najeriya.
Majalisar ta amince da kudirin nan take a zamanta na ranar Alhamis.
Wannan karin kasafin kudi, an bijiro da shi ne tun a lokacin mulkin shugaban Buhari.
Shugaba Bola Tinubu ya roƙi ‘yan Majalisar Tarayya cewa zai so su yi wa Dokar Kasafin 2022 gyara, domin ya samu damar raba wa marasa galihu tallafin naira biliyan 500.
Roƙon ya zo cikin wata takarda da Shugaban Ƙasa ya aika wa Shugaban Majalisar Tarayya, Tajuddeen Abbas, a ranar Laraba.
Shugaban ƙasa ya ce zai cire tallafin daga cikin ₦819,536,937,813.
Waɗannan adadin kuɗaɗen tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya shigar da su a kasafin 2022 domin Ayyuka a wurare da ambaliyar ruwan sama ya lalata.
A baya su ma Gwamnonin Najeriya sun ce za su taya gwamnatin Tarayya samar wa talakawa hanyoyin rage raɗaɗin talauci.
Gwamnonin ƙasar nan sun tabbatar cewa za su gaggauta samar wa talakawa tallafin rage masu raɗaɗin tsadar rayuwa, bayan cire tallafin fetur da aka yi, wata ɗaya da ya wuce.
Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya bayyana haka, bayan tashin su daga taron da su ka yi da Shugaba Bola Tinubu, ranar Alhamis a Legas.
Ya ce Gwamnoni za su taya Gwamnatin Tarayya fitar da al’ummar ƙasar nan daga wahalhalu.
‘Yan Najeriya na fama da matsanancin ƙuncin rayuwa, bayan Buhari, tsohon shugaban da aka zaɓa don ya sauƙaƙe tsadar fetur, kayan abinci da masarufi, amma su ka nunnunka a zamanin sa.
Discussion about this post