Rundunar Sojin Najeriya dake aiki a karkashin ‘Operation Delta Safe’ sun gano tare da lalata matatun man sata guda 47 sannan sun kama barayin danyen man fetur 65 a cikin makonnin biyu da suka gabata.
Shugaban yada labarai na ma’aikatar tsaro Musa Danmadami ya sanar da haka ranar Alhamis.
Danmadami ya ce sojojin sun kara kaimi a yakin da suke yi da satar man fetur, matatun da dai sauran muggan aiyukka ta hanyar kai farmaki, yin sintiri, da dai sauran su.
Dakarun sun kama lita 186,000 na danyen mai, lita 42,750 na man fetur, man inganta injin mota lita 4,500 da lita 200 na kananzir.
An Kuma kama tankunan mai 250, rijiyar mai 32, jiragen ruwa 31, injin walda daya da injin tunkudo mai guda daya.
Ya ce dakarun sun Kuma kama harsasai 300, harsasan bindiga kiran AK-47 guda 15, wayoyin salula 211, motoci uku, kullin ganyen wiwi guda 100.
Sannan a ranar 18 ga Mayu dakarun sun kai hari gidan wani dan ta’adda a kauyen Ibas dake karamar hukumar Ahoads ta Yamma jihar Ribas.
A yankin Kudu maso Gabas Danmadami ya ce rundunar ‘Operation UDO KA’ ta kashe mutum biyar ‘yan kungiyar Biafra, ta kama wasu guda 9 tare da makamai da dama a hannun su.
A Kudu maso Yamma ya ce rundunar ‘Operation AWATSE’ ta kama ‘yan ta’ada 26 inda ta Kuma kama bindiga kirar hannu guda daya, harsasan bindiga guda uku, kwayoyin Tramadol gram 280 Da kwalaben kodin.
Discussion about this post