Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana dalilin da ya sa ta yi wa Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa jayayyar nuna rashin amincewa da kwafe-kwafen bayanan zaɓen da Atiku Abubakar da Peter Obi su ka gabatar wa kotu.
Atiku da Obi dai sun lodi tulin kwafen bayanan zaɓe wanda su ka kwafa daga na’urorin tantance masu rajistar zaɓe (BVAS), su ka riƙe wa kotu.
Sun kwafi bayanan ne daga kusan jihohin ƙasar nan har da Babban Birnin Tarayya (FCT) Abuja.
Lokacin da ake zaman yadda za a cimma matsayar yadda ɓangarorin masu ƙara da waɗanda ake ƙara za su amince a rage tsawon lokacin da za a shafe ana sauraren ƙararrakin zaɓe, lauyoyin ɓangarorin sun amince cewa ba za su tsaya su na tankiya kan shaidun da aka bayar a matsayin kwafen takardun shaida ko hujjoji, matsawar daga INEC bayanan su ke.
To sai dai kuma a zaman kotu na ranar 30 Ga Mayu, 2023, lauyan INEC Abubakar da Lauyan Tinubu Wole Olanipekun duk sun ƙi amincewa da bayanan da Atiku da Obi su ka gabatar wa kotu, duk kuwa da cewa daga kotu su ka sami bayanan.
Shi ma lauyan APC, Lateef Fagbemi ya ƙi amincewa da bayanan a matsayin hujjoji daga INEC.
A zaman ranar Juma’a, lauyan INEC Pinheiro Kemi, ya bayyana wa kotu cewa Atiku da Obi bs su ƙalubalanci zaɓukan da aka yi a yankunan da su ka kwafo bayanan zaɓe daga yankunan a lokacin da aka kwafo bayanan ba.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Tinubu da INEC sun ƙi amincewa da tulin kwafe takardun da Atiku ya kwafo daga BVAS na jihohi 32 ya damƙa wa kotu.
A ranar Laraba ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙalubalanci lodin tulin kwafe-kwafen bayanan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023, waɗanda ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Abubakar ya kwafo daga na’urorin BVAS daga jihohi 32.
Atiku ya gabatar wa Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa da ke zama a Abuja kwafe-kwafen bayanan.
Haka nan ita ma Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta nuna jayayya da rashin amincewa Atiku Abubakar ya gabatar wa kotu kwafen takardun a matsayin shaida.
Takardun waɗanda lodi ne mai tarin yawa, Atiku Abubakar a kwafo su ne da na’urar tantance masu rajistar zaɓe (BVAS) daga jihohi 32, amma banda Kaduna, Kano, Katsina da Legas.
Tinubu wanda ya yi nasara a zaɓen 2023, ƙarƙashin APC, ya na ta gaganiya da faɗi-tashin kare kujerar sa, domin ganin kotu ba ta ƙwace ta bai wa Atiku da ya yi na biyu ba, ko kuma Peter Obi, wanda ya yi na uku.
Su biyun dai sun maka APC, Tinubu da INEC a kotu, kowanen su na iƙirarin a soke zaɓe a sake sabo, ko kuma a ba shi nasara.
Yayin da batun gabatar da shaidu ya bijiro a Kotu a ranar Laraba, lauyan Atiku Eyitayo Jegede, gabatar wa kotun da shirgin kwafe-kwafe na bayanan da ya kwafo daga INEC.
Babban Lauya (SAN) Jegede, ya roƙi kotu ta karɓi bayanan a shigar da su a matsayin shaidu a ƙarar da Atiku da PDP su ka maka INEC, Tinubu da APC a kotu.
Amma lauyan Tinubu Emmanual Ukala da Lateef Fagbemi da lauyan INEC Kemi Pinhiero, duk sun na ƙin amincewa da gabatar da kwafen takardun.
Atiku bai ma tsaya a nan ba, sai da ya gabatar da sakamakon zaɓe Jihar Abiya, Arewa maso Gabas ta Najeriya.
Ya kuma kwafo wasu takardun sakamakon zaɓe daga jihohin Bayelsa, Kaduna’ da Ogun.
Discussion about this post