Alhamis, 29/06/2023
Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu alaikum
Yaku bayin Allah, Allah Subhanahu wa Ta’ala ne da kansa, yayi umurni da a taimakawa marasa hali a cikin wannan al’ummah. Wasu bayin Allah managarta sun amsa wannan kira na Allah, shi yasa aka wayi ba dare ba rana, suna ta fadi-tashi da kokarin ganin sun taimaki bayin Allah da dan abunda ya hore masu. Wasu kuwa sun ki amsa wannan kira na Allah, sun boye, tare da taskance abunda Allah ya basu. Sai aka wayi gari babu mai amfana dashi, daga su sai ‘ya ‘yansu.
Yaku ‘yan uwana masoya, wallahi daga cikin wadanda suka amsa wannan kira na Allah wurin taimakon bayin Allah, akwai Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Muhammad Sanusi II, Sarkin Kano na goma sha hudu.
Wannan bawan Allah, ni dai ina ganin mutane masu kyauta da alkhairi da taimakon bayin Allah mabukata, kuma suna nan da yawa cikin wannan al’ummah, amma dai a gaskiya, ni ban gaba ganin irin sa ba.
Muhammad Sanusi II, mutum ne da baya tsoron talauci, domin ya riga ya fahimci wannan duniya da abunda yake cikin ta. Yasan cewa duniya ba komai bace, kuma abunda ka bayar shine naka. Ya fahimci cewa, ko mutum ya bayar ko bai bayar ba, abunda ya mallaka zai kare. Duk abunda ya shigo hannun Mai Martaba, to ina mai tabbatar maku da cewa wannan abun na jama’ah ne. Bai taba samu yaci shi kadai ba, kullun aikinsa shine ciyar da bayin Allah. Bai taba gudun mabukata ba. Bai taba kokarin cewa daga shi sai ‘ya ‘yansa ba. Bai taba boye abunda Allah ya bashi ba, idan akwai zai bayar idan babu zai baka hakuri har zuwa lokacin da Allah ya kawo.
Mai Martaba ya dauki nauyin karatun bayin Allah, wadanda Allah ne kadai yasan iyakarsu. Ya basu sukolashif da sauransu, saboda suyi karatu, su zamo ‘ya ‘ya nagari, wadanda zasu kawo ci gaba cikin wannan al’ummah.
Mai Martaba Sarki ya taimaki masu cutar kansa marasa iyaka, ya taimaki marasa lafiya daban-daban, wadanda Allah ne kadai yasan iyakarsu.
Sarki ya taimaki dimbin malaman makaranta saboda sanin muhimmancin malamai a cikin al’ummah. Ya taimakawa karatun mata, saboda sanin mata ginshikai ne a cikin al’ummah, kuma har yanzu yana kan taimakawa.
Kuma Khalifah Muhammad Sanusi II ya kasance shi wani irin mutum ne mai yin duk abunda zai yi domin Allah. Baya so a bayyana duk wani nau’in taimako da agaji da yake bawa al’ummah.
Wallahi duk wani bayani ko sako ko sanarwa, na wasu abubuwa da yake yi game da taimakawa bayin Allah, Allah ya sani, muna yi ne ba da saninsa ba. Mune kawai muka ga dacewar yin hakan. Wannan kuwa ba domin komai ba, sai don saboda wasu dalilai, da kuma kokarin toshe bakin makiya, makirai, magauta da mahassada, wadanda har kullun suke bibiyar wannan bawan Allah da sharri iri-iri daban-daban.
Amma in domin sa ne, wallahi shi kam, har kullun cewa yake yi, Allah da muke yi dominsa ya sani.
Yaku ‘yan uwana masu daraja, a cikin irin ayukkan alkhairai da Mai Martaba Sarki yake gabatarwa domin bada gudummawa wurin taimakon bayin Allah, da kuma bin umurnin Allah da manzonsa (SAW), a yau ranar alhamis, 29 ga watan shida,
Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Muhammad Sanusi ll, bisa jagorancin amintaccen kaninsa, wato Mai girma Falaki, Alhaji mujtaba Abubakar Abbah, ya gudanar da rabon tallafin naman babbar Sallah, karkashin shahararriyar kungiyar nan, wadda aka kafa ta domin gudanar da ayukkan ci gaban al’ummah daban-daban, wato Muhammad Sanusi ll Foundation, ta raba naman Layyah ga ‘yan uwanmu marasa karfi, bayan rabon dimbin raguna da shanu, wadanda Allah ne kadai yasan adadin su.
An dade ba tun yau ba ana gudanar da ayukkan alkhairi a karkashin wannan kungiya. Kuma wannan kungiya, ina mai yi maku rantsuwa da Allah cewa, ko shi Mai Martaba Sarki da ya kafa ta, ko aka kafa ta da sunansa, bai iya kididdige ayukkan data gabatar na alkhairi a cikin al’ummomi daban-daban.
Don haka, babu abunda zamu ce sai addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya saka wa Mai Martaba Sarki da mafificin alkhairi duniya da lahira. Allah yasa sakamakon wannan aiki a mizaninsa na ayukkan alkhairi, shi da dukkanin masu taimaka masa wurin gudanar da wannan aiki, amin.
Allah ya taimaki Sarki, ya kara masa lafiya, imani da nisan kwana, kuma Allah ya maimaita muna, amin.
Dan uwanku, masoyinku ne, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi Najeriya. Za’a iya samun Imam a wannan lambar waya kamar haka: 08038289761.
Discussion about this post