Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi hakuri yayin da yake kaddamar da wasu sauye-sauye domin kawo sauyi a kasar.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyar nuna godiya ga Alake na Egbaland, Adedotun Gbadebo, a fadarsa da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
A cikin tawagarsa akwai mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila da mai magana da yawun shugaban kasa, Dele Alake.
Da yake jawabi a fadar Alake dake Abeokuta, shugaban ya godewa shugabannin jam’iyyar APC bisa nasarar da jam’iyyar ta samu a jihar a zaben shugaban kasa.
Sannan Tinubu ya yi alkawarin cewa nan ba da dadewa ba ƴan Najeriya za su fara samun kyawawan sauye-sauye ma su ma’sna wanda za du yi alfahari da su.
Ya ce duk da cewa ba gaggawa ya ke yi ba na ganin ya cika alkawuran yakin neman zabe da ya yi ba, ya roki ‘yan Najeriya da su hakura da ya ke yi sannu a hankali, domin ganin ya kawo cigaba da za ayi alfahari da su a kasar nan.
Najeriya ita ce kasa ta kuma da ita nake alfahari da, na taba zama ɗan gudun hijira a wata kasa, abun ba a cewa, a nan ne na san cewa Kowa Ya Bar Gida, Gida Ta Barshi.
Discussion about this post