An tashi taron matsalar ƙarin farashin man fetur tsakanin wakilan gwamnatin tarayya da Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa baram-baram.
An yi taron a Fadar Shugaban Ƙasa, wanda Shugaban NNPCL, Mele Kyari, hadimin Shugaban Ƙasa Dele Alake, Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta TUC, Festus Osifo da wasu jami’an gwamnati.
Cikin sanarwar da NLC ta fitar bayan tashi daga taron, ta bayyana cewa ita da ‘yan Najeriya ba za su amince da wannan mahaukacin ƙarin kuɗin fetur ba.
NLC ta ce an yi ƙarin ba shiri, kuma an shammaci ‘yan Najeriya da ba-zatar ƙarin fetur.
A ranar Laraba dai NNPCL ta umarci dukkan gidajen mai su koma sayar da fetur daga N480 zuwa N570.
An yi wannan mahaukacin ƙarin ne daga N193 da ake sayarwa a lokacin da aka yi ƙarin.Kakakin NNPCL, Garba Deen Muhammd ya ce ya ce an yi ƙarin kuɗin ne bisa haƙiƙanin yadda kasuwa ta ke a halin yanzu.
NNPCL ta yi sanarwar kwana biyu bayan Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cire tallafin fetur baki ɗaya a ranar Litinin, lokacin rantsar da shine.
Tuni dai tsohuwar gwamnatin Buhari ta bayyana cewa bai yiwuwa a riƙa biyan tallafin fetur, ganin yadda gwamnati ke kashe naira biliyan 400 duk wata su na tafiyar wajen biyan tallafin fetur.
Dama kuma a cikin kasafin 2023, an tsara cewa batu biyan tallafi tun daga watan Yuni da ya kama yau.
Farkon wannan makon kuma NNPCL ta bayyana cewa ta na bin gwamnatin tarayya bashin naira tiriliyan biyu na kiɗin tallafin da ta biya, amma Najeriya ba ta biya ba, har Buhari ya sauka daga mulki a ranar 29 Ga Mayu.
A na ta bayanin NLC ta ce ya kamata gwamnatin Tinubu ta tuntuɓi ‘yan Najeriya kafin ta yi gaggawar cire tallafin fetur.
Discussion about this post