A ranar Laraba ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙalubalanci lodin tulin kwafe-kwafen bayanan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023, waɗanda ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Abubakar ya kwafo daga na’urorin BVAS daga jihohi 32.
Atiku ya gabatar wa Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa da ke zama a Abuja kwafe-kwafen bayanan.
Haka nan ita ma Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta nuna jayayya da rashin amincewa Atiku Abubakar ya gabatar wa kotu kwafen takardun a matsayin shaida.
Takardun waɗanda lodi ne mai tarin yawa, Atiku Abubakar a kwafo su ne da na’urar tantance masu rajistar zaɓe (BVAS) daga jihohi 32, amma banda Kaduna, Kano, Katsina da Legas.
Tinubu wanda ya yi nasara a zaɓen 2023, ƙarƙashin APC, ya na ta gaganiya da faɗi-tashin kare kujerar sa, domin ganin kotu ba ta ƙwace ta bai wa Atiku da ya yi na biyu ba, ko kuma Peter Obi, wanda ya yi na uku.
Su biyun dai sun maka APC, Tinubu da INEC a kotu, kowanen su na iƙirarin a soke zaɓe a sake sabo, ko kuma a ba shi nasara.
Yayin da batun gabatar da shaidu ya bijiro a Kotu a ranar Laraba, lauyan Atiku Eyitayo Jegede, gabatar wa kotun da shirgin kwafe-kwafe na bayanan da ya kwafo daga INEC.
Babban Lauya (SAN) Jegede, ya roƙi kotu ta karɓi bayanan a shigar da su a matsayin shaidu a ƙarar da Atiku da PDP su ka maka INEC, Tinubu da APC a kotu.
Amma lauyan Tinubu Emmanual Ukala da Lateef Fagbemi da lauyan INEC Kemi Pinhiero, duk sun na ƙin amincewa da gabatar da kwafen takardun.
Atiku bai ma tsaya a nan ba, sai da ya gabatar da sakamakon zaɓe Jihar Abiya, Arewa maso Gabas ta Najeriya.
Ya kuma kwafo wasu takardun sakamakon zaɓe daga jihohin Bayelsa, Kaduna’ da Ogun.
Discussion about this post