Wata kungiyar goyon bayan Bola Tinubu, zababben shugaban Najeriya, ta isa kotun koli da ke Abuja gabanin yanke hukuncin ranar Juma’a kan karar da ke neman a soke Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa da kuma shirin rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu.
Mambobin wannan kungiya sun yi cincirindo a kusa da babbar kotun sun ta yin wakar nuna goyon baya ga Tinubu da Mataimakin sa.
Tare da su tsohon dan tsageran yankin Neja Delta, Asari Dokubu, wanda ya zauna ya na sauraren a yanke hukuncin karar.
Jam’iyyar PDP ce ta shigar da kara a gaban kotun inda take neman a soke Bola Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu kan zargin da ake masa na tsayar da abokin takararsa, Kashim Shettima bai dace ba.
Hakazalika jam’iyyar ta gabatar da batun a cikin karar da ta shigar gaban kotun zaben shugaban kasa domin kalubalantar nasarar da Tinubu ya samu a zaben.
Sai dai kotun ta yi watsi da wannan kara a hukuncin da ta yanke a ranar juma’a.
Alkalai biyar karkashin jagorancin Inyang Okoro sun yi watsi da karar baki dayan su a ranar Juma’a.
Adamu Jauro, ɗaya daga cikin alkalan da suka yanke hukuncin, ya ce PDP ba ta da hurumin shigar da kara a kan abubuwan da ya shafi gudawar cikin gida na wata jam’iyya.
“Ya kamata a lura cewa babu wata jam’iyyar siyasa da za ta iya kalubalantar zaben wata jam’iyyar siyasa.
“Jam’iyyar siyasa ba ta da ‘yancin kalubalantar ayyukan zaɓen fidda gwana na wata jam’iyya.
Discussion about this post