Wani dalibin kwalejin kimiya da fasaha ta gwamnatin tarayya dake Ilaro jihar Ogun, Samuel Adegoke ya kashe kansa ta hanyar kwankwaɗar maganin kwari bayan ya an cinye masa kuɗin makaranta da na abokin sa a caca
Lamarin ya auku ne yayin da ɗalibin ke shirin fara rubuta jarabawar farko na zangon kararu ta biyu a kwalejin.
Bayanai sun nuna cewa Adegoke ya saci kudin makarantar wani da suke zama a daki daya ya haɗa su duka ya buga cacan da su.
Rajistarar kwalejin, Sola Abiala shima ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Abiala ya ce ya samu labarin abin da ya faru yayin da aka bayyana masa cewa daya daga cikin daliban makarantan mai suna Samuel Adegoke ya kashe kansa bayan an cinye kuɗin makarantar sa da na abokin sa da ya sauke bai sani ba ya kuma je ya buga caca da su aka cinye.
“Na faɗi wa mahaifin sa abin da ya faru inda shi mahaifin ya ce idan da ya san haka ne da ya aiko wa dansa kudin ya biya a maimakon ya kashe kansa domin shi ne dan sa na farko cikin yayan sa.
“Mahaifin ɗalibin ya roki hukumar makarantar su bizine ɗan saboda ba zai iya daukar gawarsa ba ya kai shi gida saboda kashe kansa da yayi. Ya hakura har da gawar ma.
Discussion about this post