Yin magana akan wayar tafi da gidanka na tsawon mintuna 30 ko sama da haka a kowane mako yana da alaƙa da haɗarin hawan jini da kashi 12 cikin ɗari, in ji wani bincike da Ƙungiyar Ƙwararru, (ESC) ta buga.
Sakamakon binciken da aka buga a cikin Jaridar – Digital Health, mujallar ESC, an buga shi akan Yanar Gizo na ESC ranar Juma’a.
Binciken da Farfesa Xianhui Qin na Jami’ar Kiwon Lafiya ta Kudancin Guangzhou na kasar Sin ya rubuta, ya ce yana da kyau a takaita kiran wayar hannu don kiyaye lafiyar zuciya.
“Yawan mintunan da mutane ke ɗauka suna magana akan wayar hannu na da matukar illa ga lafiyar zuciya sannan yana kara hawan jini.
Sai dai kuma har yanzu sai an zurfafa bincike domin kara samun tabbatar da sahihancin wannan bincike.
Akalla mutum biliyan 1.3, masu shekaru 30 zuwa 79 a duniya, suna da hawan jini.
Wayoyin hannu suna fitar da makamashi da ke haddasa hauhawar hawan jini bayan ɗan gajeren lokaci.
Qin ya ce binciken ya yi nazari kan alakar da ke tsakanin kira da amsa waya da kuma tashin hawan jini, ta hanyar amfani da bayanai daga cibiyar Biobank na UK.
A cewarsa, an saka manya 212,046 masu shekaru 37 zuwa 73 da ba su da hawan jini a cikin binciken.
Binciken ya nuna cewa waɗanda ke yawan tsaya kan waya suna magana mai tsawo fiye da minti 30 a cikim mako guda sun fi fadawa cikin haɗarin kamuwa da tashin hawan jini.
” Wadanda ke dadewa har tsawon mintuna 30 ko sama da haka a kowane mako na cikin haɗarin kamuwa da cutar hawan jini da kashi 12 cikin 100 fiye da waɗanda basu dadewa bisa waya.
Farfesa Qin ya ce duk da ana zufafa bincike da nazari akan haka, mutane su rika taƙaita maganganun da suke yi a kan yawar hannu domin kauce wa haɗarin da ke tattare da yin hakan.
Discussion about this post