Zababben shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi alhinin tunawa da marigayi tsohon shugaban kasa Umaru Yar’aduwa da da ya rasu shekaru 13 da suka wuce a irin rana ta yau, wato 5 ga Mayu.
A yau, kamar kullum, ina tunawa da abokina kuma dan uwana na kud-da-kud a fafutukar tabbatar da dimokuradiyya da shugabanci na gari a Najeriya, wato Marigayi tsohon shugaban kasa Umaru Musa ‘Yar’aduwa, wanda ya rasu a rana irin ta yau shekaru 13 da suka gabata.
Ranar 5 ga Mayu, 2010 mai yiwuwa ya daɗe amma, ga wasunmu, raunin har yanzu sabo ne. Muna tunawa da ranar kamar yadda muke tunawa da irin rayuwa mai cike da abin tunawa da dimbin alkhairai da marigayi Umaru Yar’adua ya yi.
A matsayina na abokinsa kuma abokin gwagwarmayar siyasa bazan manta rikon gaskiya da yake dashi ba,sannan kuma da kishin kasa, da nuna kwarewa a harkar ayyukan sa tun daga lokacin da ya zama gwamnan a 1999 – 2007 da kuma shugabancin Najeriya da yayi daga 2007- 2010.
A yayin da nake shirin karbar ragamar shugabancin kasar nan a ranar 29 ga watan Mayu, na kuduri aniyar yin koyi da nagartattun shuwagabanni irin su marigayi Umaru ‘Yar’aduwa wadanda suka nuna kololowar nagarta da sadaukar da kai domin cigaban kasar mu.
Ina maka addu’ar Allah ya kyautata makwancinka, ya sa Aljanna ta zamo makomar ka, Amin.