Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda ya ce zai saka tsarin ‘Treasury Single Account’ a harkokin shige da ficen kudade jihar Katsina domin dakile hanci da rashawa.
Radda ya fadi haka ne a Lokacin da yake karanta jawabinsa na farko bayan babban alkali Musa Danladi ya rastsar da shi sabon gwamnan Katsina ranar Litini.
“Za mu shigo da tsarin TSA domin karfafa tsarin kashe kudade a jihar Katsina. Yin hakan zai taimaka wajen ganin an kashe kudaden gwamnati ta hanyoyin da suka kamata domin amfanin al’umma.
Ya ce zai yaki tabarbarewar rashin tsaro kai tsaye a jihar.
“ Yaki da rashin tsaro na daga cikin mahimman matsalolin da gwamnati na za ta fi maida hankali akan su. Zan yi amfani da karfin da doka ta bani domin na yaki mahara sannan zan hada hannu da mutane domin ganin mun kawar da rashin tsaro a jihar Katsina.
“Gwamnati na za ta taimakawa wadanda hare-haren ‘yan bindiga ya shafa a jihar.
Radda ya yi kira ga ‘yan ta’adda su tuba su mika makaman su ko su fuskanci fushin luguden gwamnati babu kakkautawa.
Gwamnan ya yi alkawarin kawo canje-canje masu amfani a jihar domin taimakon talakawa da duka mutanen jihar.
Radda ya ce gwamnatin sa za ta farfado da fannin ilimi, Kiwon Lafiya, Noma, domin kawo karshen matsalolin da ake fama da su a wadannan fannoni.
Radda ne ya gaji Aminu Bello Masari wanda ya kammala wa’adin mulkin sa ranar Litinin.
Discussion about this post