Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa ya rangada wa titin Raba sunan tsohon gwamna Nasir El-Rufai shine don jihar ta karrama shi bisa kyawawan ayyukan da yayi a jihar.
” Wannan karramawa da muka yi maka yau, an yi shi ne domin a mu saka maka bisa irin ayyukan raya kasa da ka yi a jihar Kaduna da ba a taba yin irin sa ba. A dalilin haka ya sa na canja sunan Raba Road gabadayan sa zuwa Titin Nasir El-Rufai.
” A nan nake sanar da sauya sunan titin Rabah baki daya zuwa titin Nasir El-Rufai. Na umurci hukumar raya birnin Kaduna da ta aiwatar da canjin zuwa sunan Nasir El-Rufai wanda titi ne mai tsawon kilomita 15.
” Ina cike da fari cikin aiwatar da wannan canjin suna, ganin cewa ita kanta aikin titin El-Rufai ya kirkirota wacce za ta mike har babban titin Bypass sannan ya karisa tashan jirgin kasa dake Rigasa.
Discussion about this post