A yanzu dai za a iya cewa shari’ar jayayya da nasarar Bola Tinubu ta fara zafi, domin ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP, Atiku Abubakar ya gabatar wa Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa shirgin bayanai da aka kwafo daga nau’arar tantance rajistar masu zaɓe, lokacin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
A ranar Talata ɗin nan, Atiku ya gabatar da kwafen bayanan BVAS ɗin a Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa, kwana ɗaya bayan da ɗan takarar shugaban ƙasa a LP, Peter Obi ya gabatar wa ita wannan kotu da kwafen takardun da ke tabbatar da wata kotu a Gundumar Illinois da ke Amurka, ta taɓa cin Tinubu tarar dala 460,000, saboda an kama shi ya na hada-hadar mu’ammali da muggan ƙwayoyi.
Atiku wanda ya zo na biyu, ya ɗaukaka ƙara ne saboda ya yi zargin an yi masa maguɗi a wurare da dama lokacin zaɓe.
Daga cikin maguɗin da Atiku ke zargin an yi masa, akwai rashin tattara bayanan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, zuwa Rumbun Adana Sakamakon Zaɓe.
A zaman sauraren ƙarar da aka yi yau ranar Talata, lauyan Atiku mai suna Eyitayo Jegede, ya gabatar da kwafe-kwafen takardun bayanan da ke cikin BVAS
Kotu ta karɓi kwafen takardun zargin Asiwaju ya yi harƙallar muggan ƙwayoyi.
Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa da ke Abuja ta karɓi kwafen takardun da aka shigar, waɗanda ake kafa hujja da su cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi tu’ammali da muggan ƙwayoyi, har Amurka ta ci shi tarar dala 460,000.
Kotun ta karɓi takardun a matsayin shaidu a ƙarar da Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na LP ya shigar.
Obi ya na ƙalubalantar nasarar Tinubu, inda ya ke neman kotu ta ayyana cewa shi ne ya ci zaɓe, ko kuma a soke zaɓen, a yi wani sabo baki ɗaya.
Obi ya na ƙarar cewa an tafka maguɗi a lokacin zaɓe, sannan kuma Tinubu bai cancanci tsayawa takarar zaɓe ba.
An dai rantsar da Tinubu a ranar Litinin, duk kuwa da cewa ana ci gaba da shari’ar da Obi, Atiku da APM su ka maka shi.
Za a kammala shari’un a Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa a cikin Satumba, kafin daga nan a rankaya Kotun Ƙoli.
Obi ya kafa wa Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa hujja daga dala 460,000 da Kotun Gundumar Illinois ta ci Tinubu tara, bayan kama shi da muggan ƙwayoyi a Amurka.
Wannan kwafen shaida dai shi ne mai lamba 93C 4483 da ke gaban alƙalan kotun, ƙarƙashin jagorancin Babban Mai Shari’a, Haruna Tsammani.
Haka kuma Obi ya ce takarar Kashim Shettima haramtacciya ce, domin ya fito takara wuri biyu a lokaci guda. Wato takarar sanatan Barno da kuma takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Discussion about this post