Ranar 9 Ga Yuni, 2022, mafi ƙarancin shekaru a cikin ‘yan takarar zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa a APC, mai suna Nicholas Felix, ya hau duro a Dandalin Eagle Square, Abuja lokacin zaɓen fidda gwani. Ya yi magana ya ce shi dai ya janye, ya bar wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo.
Ya nuna cewa ya janye ne, domin akwai yiwuwar cewa idan aka tsayar da Bola Tinubu takara, to Musulmi zai ɗauko mataimakin takarar sa.
“Na taso tare da Musulmai tun ina ƙarami. Su na da daɗin mu’amala, kuma har yanzu ina da abokai da yawa Musulmi. To amma dai ba daidai ba ne a ce mu tsayar da ‘yan takara Musulmi a APC, kuma a ƙasa kamar Najeriya.
Kafin nan dama kuma a wurin gangamin, ana ta tuttura wa wakilan zaɓen ‘yan takara saƙon tes cewa idan su ka zaɓi Tinubu, to Musulmi zai ɗauka mataimakin takarar sa, a yi Muslim-Muslim kenan.
Nan da nan tawagar Tinubu ta ce sharri ne ake yi wa Tinubu, ba gaskiya ba ce. Duk da haka dai sai da Tinubu ya lashe zaɓen fidda gwani, kuma kamar yadda Felix ya ce Tinubu zai ɗauki Musulmi takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa. Lamarin da ya ɓata ran miliyoyin mutane da dama a ƙasar nan.
Duk da Tinubu ba mai ra’ayin riƙau ɗin addini ba ne, hasali ma matar sa da ‘ya’yan sa duk Kiristoci ne, hakan bai hana an riƙa zargin sa cewa ya na da ajandar maida Najeriya ƙasar Musulunci.
Hakan ya sa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal da tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu dogara su ka fara yaƙi da Tinubu.
Sai dai kuma duk da saɓanin da aka samu da haushin Tinubu da ake ji, hakan bai hana shi yin nasara a zaɓen 25 ga Fabrairu ba.
Ganin yadda ta kasance, yanzu kuma an koma ana maganganun cewa ya kamata Tinubu ya biya Krisitoci bashin da ya ci na su, na ƙin ɗaukar Kirista takara.
Ta ina zai fara biyan bashin? Zai fara ne daga Shugaban Majalisar Dattawa da kuma Kakakin Majalisar Tarayya.
Duk da cewa ‘yan majalisar ne da kan su ke yin zaɓen shugabannin su, amma dai jam’iyya mai mulki ko mai rinjayen yawan mambobi ko sanatoci ta na da ta cewa a zaɓen.
To kuma APC ce ke da mafiya yawan Sanatoci har 57. Kuma ‘yan Majalisar Tarayya ta na da 162, ba su kai 181 da doka ta ce su ne ‘majority’ ba.
Kafin a zaɓi Shugaban Majalisar Dattawa da na Tarayya, tilas a duba na yanzu ‘yan zangon 2019 zuwa 2023, daga wace shiyya su ka fito? Kuma wane addini su ke.
Sanata Ahmed Lawal na Dattawa dai Musulmi ne, kuma ɗan yanki ɗaya da Kashim Shettima, mataimakin shugaban ƙasa zaɓaɓɓe.
Shi kuma Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila, shi ma Musulmi ne, ɗan jiha ɗaya da Shugaba Bola Tinubu zaɓaɓɓe. Ba zai yiwu a sake ba su shugabancin majalisa ko wani ɗan yankin su.
APC ta rasa ‘yan majalisa 19 daga Kano a zaɓen 2023. Ta rasa da dama a Gombe, Kaduna, Katsina da Osun.
A taƙaice a 2019 APC na da wakilai 211, amma a zaɓen 2023 ta na da 162.
Addinanci Da Shiyyanci A Zaɓen Shugabannin Majalisar Dattawa Da Na Tarayya:
Tunda APC ta yi Muslim-Muslim a zaɓen Shugaban Ƙasa kuma ta yi nasara, to zai kasance tilas ta biya Kiristoci bashin da ta ɗauka, ta hanyar zaɓen Kiristoci shugabannin majalisun biyu.
Tuni dai daga Kudu maso Gabas irin su Sanata Uzor Kalu, Gwamna David Umahi wanda zaɓaɓɓen sanata ne, sai irin su Osita Izunaso sun fara fitowa su na neman shugabancin Majalisar Dattawa.
Sai dai matsalar Kudu maso Gabas da wakilan ta shi ne APC ba ta samu kashi 25 bisa 100 na yawan ƙuri’u daga kowace jiha a yankin ba, a lokacin zaɓen shugaban ƙasa.
Tinubu ya samu ƙuri’u 127,605 arankatakaf a Kudu maso Gabas, jihohi biyar ɗin da su ka haɗa da Abiya, Enugu, Ebonyi, Imo da Anambra.
A wani ɓangaren kuma Kudu maso Kudu kuma irin su Godswill Akpabio da Adams Oshiomhole na harin shugabancin Dattawan Majalisa.
Kusan kowane yanki ana farautar ko dai shugabancin ta Dattawa ko ta Tarayya. Amma dai, duk yadda ta je ta dawo, akwai maganar da ba za a iya jingine ta gefe ba, wato batun a biya bashin addinancin da aka nuna a takarar Muslim-Muslim.
Discussion about this post