Wani magidanci mai suna Oyibo Moses a ranar Litini ya kai karar matarsa Joy a kotun gargajiya dake Nyanya Abuja saboda a cewar sa tana neman ta hallaka shi.
Moses wanda ke zama a Jikwoyi ya roki kotun da ta raba auren sa domin ya samu tsira da ransa.
“Da ni da gidana kullun cikin fargaba ne ke domin duk ranar da muka samu sabani da matata sai ta yi min barazanar sai ta kashe ni.
Ya ce Joy ta daina kula da shi a matsayinsa na mijinta.
“Joy bata girmama ni a matsayina na mijinta sannan ta daina girka mun abinci kwatakwata.
“Na yi kokari ganin mun sassanta kan mu amma hakan bai yiwu ba. A dalilin haka ya sa nake so a raba auren saboda na gaji da barazanar da take mun kullum sai ta gabayana, sai ta kashe ni, sai ta hallakani.
Joy ta musanta duk abin da Moses ya fadi sannan ta roki kottu kada a raba auren har yanzu tana son mijinja.
Alkalin kotun Doocivir Yawe ya shawarci ma’auratan su koma gida su sasanta tsakanin su.
Yawe ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 26 ga Afrilu.