Babu wanda zai iya ce maka ga adadin waɗanda ciwo ya kashe, ko waɗanda su na ji su na gani su ka riƙa ɗibga asara saboda matsalar ƙarancin kuɗaɗen hada-hada a tsawon lokacin da ‘yan Najeriya su ka shafe su na ɗanɗana irin ƙuncin rayuwar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya jefa su da sunan canjin kuɗi, ko sauya launin kuɗi.
Wannan matsalar ba abin bada misali ba ce, domin misalan sun yi yawa. Amma dai mun ga inda ake sayar da saniyar naira 250,000 a kan naira 70,000 kuɗi hannu.
Mu koma batun gagarimar ɓarnar da CBN ya yi wa tattalin arzikin ƙasa da su kan su ‘yan ƙasar, za a ga cewa malejin tsadar rayuwa ya cilla sama sosai a watan Fabrairu, duk kuwa da yadda jama’a su ka riƙa sayar da kayan su arha takyaf domin samun kuɗaɗen sayen abinci, sakamakon ƙarancin kuɗaɗe a hannun mutane da bankuna. Malejin Fabrairu ya cilla zuwa 21.91, tsadar da bai yi kamar ta ba shekaru 17 da su ka gabata.
Haka rahoton PMI daga Bankin Stanbic IBTC ya nuna irin halin ƙuncin da ake ciki, musamman idan aka yi la’akari da yadda ma’aikata da dama sun kasa fita zuwa wurin aiki, saboda rashin kuɗin mota a hannun su. Wannan kuwa ya haifar da cikas ga masana’antu da dama.
Babban abin damuwa dangane da tsarin da CBN ta fito da shi, shi ne yadda kusan gaba ɗayan ‘yan Najeriya ba su yi maraba da shi, ballantana su karɓe shi hannu bibbiyu.Da dama na ganin akwai siyasa a cikin batun sauya launin kuɗin.
Sauya launin kuɗi ba wani aibi ba ne, amma hanyar da aka bi aka ƙaƙaba shi, da kuma lokacin da aka shigo da shi, ya sa mutane ba su gamsu da shi ba.
An ɓata lokaci, an yi asarar dukiyoyi, rayuka, kuma daga baya Kotun Ƙoli ta bada umarnin a maida tsoffin kuɗaɗe a hannun jama’a.
Yayin da ake cikin wannan halin, kada a mata kuma Gwamnatin Tarayya ta ciwo bashin Dala Miliyan 800, don ta raba wa faƙirai kuɗin tausar-ƙirjin fargabar tsadar rayuwa idan an cire tallafin fetur daga watan Yuni.
Alamomi daga Gwamnatin Tarayya sun nuna tabbas marasa galihu za su ɗanɗana kuɗar tsadar rayuwa daga watan Yuni zuwa ‘illa ma sha-Allahu’, yayin da an kammala shirin janye tallafin fetur, lamarin da zai sa tsadar sa ta sa da yawan masu motocin hawa za a jingine ababen zirga-zirgar na su, saboda tsadar fetur.
Dalilin haka ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta fara kinkimo bashin Dala Miliyan 800 daga Bankin Duniya, domin ta raba wa marasa galihu ‘yar la’adar tausaya masu dangane da mawuyacin halin rayuwar da za au afka nan gaba daga watan, idan an cire tallafin fetur.
Bashin wanda babu ruwa a ciki, wato a Turance ‘World Bank Facility’, za a raba kuɗaɗen ne ta hanyar tuttura wa marasa galihu miliyan har su Miliyan 50, domin a rage masu raɗaɗin ƙuncin rayuwar da za su afka nan gaba kaɗan.
Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa da Fadar Shugaban Ƙasa, ranar Laraba, a Abuja.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya jagoranci taron.
Zainab ta ce za a fara raba wa talakawa ta hanyar tuttura masu a asusun bankunan su, amma sai bayan an cire tallafin a watan Yuni tukunna.
Ta ce wannan Dala Miliyan 800 ba ita kaɗai ce za a raba masu ba, akwai sauran wani bashin ya na tafe, wannan somin-taɓi ne kawai.
Ta ce tuni akwai rajistar gidajen faƙirai, matalauta da marasa galihu har miliyan 10, waɗanda ta kintata yawan jama’ar da ke cikin lissafin ƙididdigar za su kai mutum miliyan 50. Ta ce waɗannan adadin duk sunayen su na cikin Rajistar Tattara Ƙidayar Marasa Galihu ta Ƙasa.
Zainab ta ce gwamnati a shirye ta ke ta rage wa marasa galihu raɗaɗin tsadar rayuwar da za su fuskanta nan gaba, ta wasu hanyoyi ba sai ta hanyar tura masu kuɗaɗen cefane ta asusun ajiyar su na bankuna ba.
“Ƙungiyar Ƙwadago ma akwai yiwuwar ta shigo da tsarin sayen motocin sufuri masu yawan gaske, domin rage wa ma’aikata da marasa galihu tsadar kuɗin mota nan da ɗan wani lokaci idan an janye tallafin fetur.
Discussion about this post