Gwamnatin Kaduna ta saka dokar hana walwala na awa 24 a unguwannin Nasarawa da Tirkaniya dake karkashin karamar hukumar Chikun bayan kashe wasu mutum biyu da a kayi a dalilin rikishin yan kwaya.
Gwamnatin ta saka dokar hana walwalan ne domin hana barkewar rikici a yankin.
Kwamishinan tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya sanar da haka ranar Litini.
Aruwan ya ce gwamnati ta yanke wannan hukunci bayan ta tattauna da manyan dakarun tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda da SSS sannan da shugabannin gargajiya dake unguwan Sabon Gari.
“Dokar ya ya hada da hana bukukuwan Kidan Bishi, Kidan Gala da yawon farauta da mutane ke yi a yankin.
“Dokan ya kuma haramta harkallar muggan kwayoyi a unguwannin Nasarawa da Sabon Nasarawa.
“Baya ga mutane biyu din da aka kashe wasu mutum shida sun ji rauni, mutane sun yi asarar kayan su a dalilin harin kuma jami’an tsaro sun kama wasu mutum uku da ake zargin suna da hannu a kisar wadannan mutane.
“ Gwamnan Nasir El-Rufa’I ya yaba da kokarin da sojoji da ‘yan sanda suka yi wajen dakile hatsaniyar kafin ya game gari.
Aruwan yace gwamna El-Rufai ya bada umarnin a gudanar da binciken mai zurfi don gano wadanda suka tada wannan rikici sannan a tabbata an hukunta su kamar yadda Gwamnan nasir El-Rufa’I ya yaba da kokarin da sojoji da ‘yan sanda suka yi wajen dakile hatsaniyar kafin ya game gari.
.
Discussion about this post