Zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya mika ta’aziyyar sa ga Aminu Dantata bisa rashin maidankin sa da aka yi a karshen wannan mako.
A sanarwa da ta fito daga ofishin yada labaran zababbaben shugaban kasan, Tinubu ya ce wannan rashi ne ba ga shi kadai ba wato Dantata da Iyalan sa, rashi ne ga kowa da kowa musamman wadanda ke da alaka ta kasuwanci da dangantaka da attajirin da iyalan sa.
” Ina mika ta’aziyya ta ta musamman ga Dantata da iyalan sa gaba daya. Da fatan Aljannatul Firdausi ta zamo makomar ta. Ina rokon Allah ya baiwa iyalan mamaciyar hakurin jure wannan babban rashi da aka yi.