Gwamnatin Jihar Jigawa na sanar da jama’a cewa ta gano akwai wasu mutane ‘yan kasuwa da ma’aikatu da suka daina karbar tsoffin takardun kudi na naira N200, N500 da N1000 a fadin jihar don hada-hadar kasuwanci.
Gwamnati na so ta sanar musu cewa a jihar wadannan kudade ba su daina aiki ba har sai Kotun koli ta yanke hukunci akan karar da gwamnoni suka shigar game da dakatar da kashe wadannan takardun kudade ranar 10 ga Faburairu ba.
Wannan magana na gaban kotun koli kuma ta bada umarnin a dakatar da komai sai an yi zaman sauraren karar da ka shigar gaban ta kafinnan har a kai ga yanke hukunci.
A matsayin mu na gwamnati mai bin doka, Jihar Jigawa na daga cikin gwamnatocin jihohin da suka kai wannan kara, kuma kotu bata yanke hukunci akai ba hasali ma bisa ga umarnin kotun, ta ba da damar a ci gaba da kashe wadannan takardun kudade ne har sai an yanke hukunci akai sannan a san inda aka nufa.
Saboda haka daga nan zuwa har a wanye a Kotu, takardun kudi na Naira N200, N500 da N1000 na nan a matsayin halastattun kudade da za a rika kashe su a fadin jihar har sai kotu ta yanke hukunci.
Gwamnatin Jigawa gwamnati ce dake mutunta al’ummarta da kuma share musu hawaye akan duk wani matsi da suka shiga saboda haka gwamnatin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yin amfani da sashe na 287 (1) na Kundin Tsarin Mulki (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima) da sauran wasu dokoki domin aiwatar da umarnin Kotun Kolin Najeriya.
Dokar ta ce ” Lallai a hukunta duk wanda yaki yin biyayya ga umarnin kotun koli ko shi waye.”
Saboda haka muna yin kira ga mutanen jihar su kai karar duk wani dan kasuwa, ma’aikata ko ma’aikaci da yaki ko suka ki amsar tsoffin takardun kudi na naira N200, N500 da N1000 a fadin jihar.