Hukumar Kwastam reshen jihar Kebbi ta kama haramtattun kaya da kudin su ya kai Naira miliyan 91.5 a jihar.
Shugaban hukumar Ben Oramalugo ya sanar da haka ranar a garin Birnin Kebbi da yake wa manema labarai bayanin aiyukkan da hukumar ta yi a cikin makonnin biyu da suka gabata.
Oramalugo ya ce hukumar ta yi nasarar kama wadannan kaya a dalilin maida hankali da ta yi wajen tattare hanyoyin da suka ratsa ta dazuka da na ruwa da ta fara tun daga ranar daya ga Fabrairu zuwa yanzu.
“A tsakanin wannan lokutta hukumar ta yi Kamen haramtattun kaya daga hannun ‘yan sumogal har sai 14.
“Kayan da muka kama sun hada da jarkoki 8,975 na man fetur, buhunan shinkafa 189, buhunan diga 71, belin gwanjon kaya 42 da buhuna 36 na gwanjon takalma.
“Sauran kayan sun hada da baturan na’urar Sola 110, katan 105 na magunguna, motocin tokunbo guda 7 da jibgegiyar motar tanka daya.
“A jimla kudaden kayan da muka kama ya kai Naira miliyan 92.5.
Oramalugo ya ce duk da kokarin da gwamnati ke yi wajen samar wa mutane man fetur a farashi mai sauki wasu ‘yan fasa kauri sace man suna ketarawa kasashen dake makwabtaka da mu suna saida wa.