Gwamnatin Kebbi ta samar da Naira biliyan 1.1 tallafi ga ‘yan jihar don rage radadin rashin kudi da ake fama dashi sakamakon canjin takardun kudi da aka afka a fadin kasar nan
Sakataren gwamnatin jihar Babale Umar-Yauri ya sanar da haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a garin Birnin Kebbi.
Umar-Yauri ya ce gwamnati za ta fara raba kudaden ba tare da bata lokaci ba wa ma’aikatan gwamnati, manoma, masu motocin haya da asibitoci.
Ya ce za a raba miliyan 200 ga manoma masu noman rani, miliyan 50 ga kungiyar masu motocin haya, miliyan 20 ga ‘yan acaba, miliyan 10 ga masu Keke NAPEP.
“Raba kudaden zai taimaka wajen rage wahalar rashin kudi da mutane ke fama da shi sannan da bunkasa aiyukkan noma musamman yadda gwamnati ta mai da hankali a kai.
Umar-Yauri ya ce gwamnati za ta raba Naira miliyan 200 wa manyan aibitocin da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a jihar domin ganin mutane sun samu kulan da ya kamata ko suna da kudi ko babu.
“Za Kuma a yi amfani da wani kaso na kudin domin samar da magunguna da sauran kayan aiki domin asibitoci da cibiyoyin lafiya a jihar.
“Gwamnati ta ware Naira miliyan 350 domin siyo shinkafa da za a rika siyar wa mutane a rabin farashin da ake siyarwa a kasuwa.
Umar-Yauri ya ce gwamnati za ta ci gaba da tattaunawa da mutane tare da tsara hanyoyin rage wahalhalun da mutane ke fama da su a afadin jihar.