A wani jawabi wanda fito-na-fito ne da Gwamna El-Rufai ya yi da Shugaba Muhammadu Buhari, gwamnan na Kaduna ya bayar da umarni a ci gaba da karɓar naira 500 da naira 1000 a Jihar Kaduna.
Ya bayar da wannan umarnin a cikin jawabin da ya yi wa al’ummar jihar a ranar Alhamis da dare.
A cikin jawabin, El-Rufai ya ce an ƙirƙiro canjin kuɗi ne don kawai a hana Bola Tinubu na APC yin nasara a zaɓen shugaban ƙasa, wanda za a yi a ranar 25 ga Fabrairu.
Ya ce shigo da tsarin canjin kuɗi rashin tunani ne, domin ya haifar da matsanacin ƙuncin rayuwa ga jama’a, musamman talakawa.
“Abin takaicin shi ne waɗanda canjin ya fi ƙuntata wa su ne talakawan da su ka zaɓe mu. Canjin ya na yin mummunar barazana ga jin daɗin rayuwar su.
“Jama’a sun shiga wani mawuyacin hali, saboda a yanayin da ake, kusan ƙwacen kuɗaɗe za a ce banki ya yi masu. Saboda ga kuɗaɗen su a banki amma ba su iya cira su sayi abinci, ko su biya bukatun yau da kullum na dole a cikin gidajen su.
El-Rufai ya ce an yaudari Shugaba Buhari kuma Gwamnan CBN da muƙarraban sa ne su ka yaudari Shugaba Buhari, inda ya yarda da su wai tsarin an shigo da shi ne don magance waɗanda su ka ɓoye maƙudan kuɗaɗe domin sayen ƙuri’u a ranar zaɓe.
Haka kuma ya ce wasu ‘yan cikin APC su ka karɓi tsarin canjin hannu bibbiyu, saboda sun faɗi a zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa, wanda su ke so ba shi ne ya yi nasara ba. Ya ce shi ya sa su ke ta gaganiyar ganin sun kayar da APC a zaɓen shugaban ƙasa.
“An ƙirƙiro wannan tsarin canjin kuɗi ne bayan Bola Tinubu ya yi nasarar lashe zaɓen fidda gwani, amma kuma ya ƙi ɗaukar na su a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.
“Saboda haka mu dai a jihar Kaduna ina bada umarnin a ci gaba da karɓar tsoffin kuɗaɗe har sai Kotun Ƙoli ta bada umarnin daina karɓa tukunna. Kuma duk masu kantinan da su ka ƙi karɓar tsoffin kuɗi, za’a gurfanar da su a hukunta su.”
El-Rufai ya tabbatar wa masu tsoffin kuɗaɗe cewa ba za su yi asarar kuɗaɗen su ba.