Gwamnan jihar Ribas, Nysome Wike ya bayyana cewa ƴan Najeriya da ita kanta Najeriyar na Bukatar Bola Tinubu cikin gaggawa dubi da halin da kasar ta shiga
Hakan na nuna lallai akwai kyakkyawar fahimta tsakanin Tinubu da Wike da har zai ya furta kalamai irin haka ha ɗan takarar da ba na jam’iyyar da yake ba.
Tinubu ya ziyarci Wike a ofishin sa dake garin Fatakwal, Babban birnin jihar Ribas a yayin da ya halarci gangamin kamfen na jam’iyyar.
Sai dai kuma ya gargaɗi jam’iyyar APC cewa kada su kashe kuɗin su a jihar ma wani ɗan takara na jam’iyyar domin ba zai ci ba, tun daga kasa har sama.
Hakan na nufin alakar Wike da goyon bayan sa a kan Tinubu ya tsaya.
Sannan kuma ya kara da cewa abinda ya sa ya ke wa Tinubu fatan Alkhairi shine don adalci ba aka yi wurin zaɓen sa ɗan takara da jam’iyyar ta yi.
” Mu gwamnoni biyar ba PDP, burin mu ke nan kuma matakin da muka ɗauka ke nan, duk inda ba ayi adalci ba, ba mu tare da wannan tafiya.
Ranar 25 ne ƴan Najeriya za su fita domin kaɗa kuri’a ga ɗan takarar su a zaɓen shugaban kasa da na majalisun tarayya a kasar nan.
Bola Tinubu na APC, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP ne ƴan takarar da ke kan gaba a zaɓen dake tafe.