Kotun majistare dake Kafanchan jihar Kaduna ta yankewa Ola Habila mai shekaru 46 da kanwarsa Joy mai shekaru 30 hukuncin zama a kurkuku bayan sun an same su da laifin satar Naira 700,000 kuɗin matar Habila, Janet.
Hukumar Sibul Difens NSCDC ta kama Habila da Joy bayan Janet ta kai kara ofishin jami’an tsaron ranar 12 ga Janairu.
Jami’in tsaron da ya shigar da karan Marcus Audu ya ce kudin Janet ya bace a ranar da Habila da Joy suka watsar mata da kaya a lokacin da saɓani ya shiga tsakanin su suka kaure da fada.
“Mun tsare su bisa ga laifin sata, tada hankalin jama’a, hana jami’in tsaro yin aikinsa da sauran su.
Sai dai kuma Habila da Joy sun karyata laifukan da ake zargin su da su a kotun.
Alkalin kotun Michael Bawa ya yanke hukuncin daure Habila da Joy a kurkuku sannan za a ci gaba da shari’a ranar 2 ga Faburairu.