Wani magidanci mai suna Mustapha Abdulrasheed mai shekaru 35 ya roki kotun Grade 1 dake Kubwa Abuja da ta raba auren dake tsakanin kanwarsa matarsa Amina Hamisu da mijinta Ibrahim Isyaku sanoda rashin kula da baya wa mata.
Abdulrasheed ya bayyana a kotun cewa Amina ta auri Isyaku shekara 12 da suka wuce kuma sun haifi ‘ya’ya uku tare amma tun daga wannan lokaci ya daina kula da ita da ƴaƴan su.
“Tun bayan auren Isyaku ya koma zama a Abuja ya bar iyalensa a kauye ba tare da yana zuwa ba ko ya turo kudin abinci ba.
“Da ‘yar Uwar Amina wato matata kenan ta je kauyen ta ga irin bakin wahalar da ‘yar uwarta ke sha ta dauko ta ta dawo da ita zama a gidana.
“A lokcin da Amina ta dawo gida na da zama ta haifi ‘ya’ya biyu sannan tana dauke da cikin Wani dan.
“Yanzu ɗan ya kai wata biyar kuma har yanzu Isyaku bai zo yabtafi da iyalan sa ba.
“Na gano cewa Isyaku baya girmama iyayen matarsa hakan ya sa nake so a raba auren.
Isyaku ya musanta duk abin da sirikinsa ya faɗi a kotu yana mai cewa Abdulrasheed bai taba zuwa gidan sa ya ga ko yana kula da iyalensa ko baya kula da su ba.
Alkalin kotun Yahaya Sheshi ya yanke hukuncin za a ci gaba da shari’a ranar 2 ga Faburairu.
Discussion about this post