Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta bayyana cewa ‘yan bindiga bisa babura ranar Juma’a sun yi garkuwa da daliban makarantar firamare na LEA dake kauyen Alwaza a karamar hukumar Doma.
Kakakin rundunar Ramhan Nansel ya sanar da haka wa manema labarai a garin Lafia.
Nansel ya ce daliban da aka sace ba su wuce ‘yan shekaru bakwai zuwa takwas ba sannan an yi garkuwa da su ne yayin da suke hanyar zuwa makaranta da safe da misalin karfe 7:30.
Ya ce jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da ‘yan banga sun fara yin bincike domin ceto daliban.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Maiyaki Muhammed-Baba bayan ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce rundunar na bin sawun maharan domin ceto daliban ba tare da an ji musu rauni ba.
Nansel ya ce rundunar ta tattauna da hukumar makarantar da Iyayen daliban da aka yi garkuwa da su.
Ya yi kira ga mutane da su taimaka wa rundunar da duk bayanin da suka san zai taimaka wajen ceto daliban da aka yi garkuwa da su.
Discussion about this post