Ranar Litinin da rana an shiga dabur-dabur, yayin da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele ya koma aiki a Hedikwatar CBN ɗin.
Ya koma aikin ne bayan ya shafe makonni baya Najeriya a cikin yanayi na rashin tabbas ɗin takamaimen abin da ya ke yi a Amurka.
Ya bar Najeriya a lokacin da ake cewa jami’an SSS na neman sa, sannan kuma ya koma ranar Litinin jim kaɗan sai wasu rahotanni su ka ce jami’an SSS sun mamaye Hedikwatar CBN, tare da hana kowa shiga cikin harabar a matsayin ma’aikatan bankin.
Sai dai kuma Kakakin SSS Peter Afunanya ya bayyana cewa rahoton karya ce, jami’an su ba su mamaye CBN ba, a ranar 16 Ga Janairu, 2023.
Cikin makon jiya ne PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Emefiele ya laɓaɓo, ya dawo Najeriya a asirce.
Majiya kuma ta ji cewa Emefiele ya shirya barin Najeriya kwanan nan, yayin da jami’an SSS ke neman kama shi.
An ce “zai tsare ya bar Najeriya ta yadda idan ya fita halartar Taron Tattalin Arziki na Duniya (WEF), to daga can ba zai dawo ba.”
Emefiele ya dawo yayin da ake shirin taron Kwamitin Tattauna Tattalin Arziki (MPC), wanda za a gabatar ranar 24 Ga Janairu.
Wannan taron tsare-tsaren dai shi ne zai magana a kan makomar jidalin da sauyin kuɗi da sauran matsalolin da su ka shafi tattalin arziki da kuma darajar Naira.
Abin da zai fi ɗaukar hankalin jama’a shi ne yadda za a ƙarke da Emefiele, dangane da zarge-zargen salwanta ko karkatar da tiriliyan 89 da Honorabul Gudaji
Kazaure ya yi masa.
Discussion about this post