Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Bayin Allah masu daraja, Annabi (SAW) yace:
“Tilawar Alkur’ani Mai girma da Ambaton Allah haske ne a gare ka a doron ƙasa, kuma taska ne gare ka a sama.” [Sahihut-Targhib]
Imam Ibn Al-Qayyim (Rahimahullah) yace:
“Duk wanda ya dawwama da godiya, to alkhairi zai ta bibiyarsa. Duk wanda ya dawwama da Istighfari za’a buɗe masa abubuwan da suke rufaffu.” [Ad-Da’u Wad-Dawa]
Imam An-nawawiy (Rahimahullah) yace:
“Mustahabbi ne mace ta aske gemu idan ya fito mata.” [Sharhu Sahih Muslim]
Annabi (SAW) yace:
“Ku halarci juma’ah, kuma ku kusanci liman, domin mutum ba zai gushe ba yana jinkirin zuwa juma’ah face anyi masa jinkirin shiga Aljannah.” [Sahihul-Jami’u]
Sheikh Ibn Uthaimin (Rahimahullah) yace:
“Ka kiyaye da yin Sallar asubahi da Sallar la’asar (cikin lokaci kuma cikin jam’i) zaka samu damar kallon fuskar Allah maɗaukaki a Aljannah ta dindindin.” [Sharhu Riyadus-Salihin]
Imam Al-Qurtubi (Rahimahullah) yace:
“Duk wanda ya zauna a majalisin masu aikata saɓon Allah da zunubi da laifi, kuma bai yi masu inkari ko nasiha ba, to yayi tarayya dasu a cikin aikata zunubin da laifin da saɓon.” [Ahkamul-Kur’an]
Imam Ibn Muflih (Rahimahullah) yace:
“Haramun ne Halartar taron sallar mushirkai (waɗanda ba musulmai ba) saboda faɗin Allah (SWT) والّذِينَ لا يشْهَدُون الزُّور.” [Al-Furu’]
Annabi (SAW) yace:
“A ranar juma’ah akwai wata sa’a (wato wani lokaci) da bawa ba zai roki Allah ba face ya amsa masa.” [Bukhari da Muslim]
Annabi (SAW) yace:
“Ku nemi sa’a (wato lokacin amsa addu’a) a ranar juma’ah bayan Sallar la’asar zuwa faɗuwar rana.” [Sahihut-Tirmizi]
Annabi (SAW) yace:
“Duk wanda ya lamunce man, wato ya kiyaye abinda yake tsakanin leɓɓansa (harshen sa) da ƙafafunsa (Al’aurar sa), na lamunce masa Aljannah.” [Sahihul Bukhari]
Imam Ibn Rajab (Rahimahullah) yace:
“Shagaltuwa da tsarkake zuciya, yafi muhimmanci sama da yawan Sallah da yawan azumi amma tare da tsatsar zuciya.” [Lada’ifil Ma’arif]
Imam Malik (Rahimahullah) yace:
“Duk wanda ya mutu akan Sunnah, to albishir a gare shi.” [Siyaru A’lamin-Nubalah]
Sheikh Al-Allamatus-Si’idi (Rahimahullah) yace:
“Alamar dace ga bawa shine ikhlasinsa ga Allah (wato yi domin Allah), da gaggawarsa wurin amfanar bayin Allah da halittun Allah.” [Tafsirus-Sa’adi]
Imam Mujahid Bin Jabr (Rahimahullah) yace:
“Ku riƙi abinda ya bayyana a gare ku (wurin yin hukunci), ku bar abinda ya ɓuya gare ku (kada kubi diddigin abinda ya ɓuya).” [Jami’ul Bayan na ad-Dabari]
Umar (RA) yace:
“Ku nisanci (tarayya da) maƙiyan Allah a idinsu da sallarsu, saboda fushin Allah na sauka akan su (a lokacin).” [Bukhari a cikin At-Tarikh]
Imam Ibn Taimiyyah (Rahimahullah) yace:
“Mumini yana farin ciki da abinda yake faranta wa muminai rai, haka yana baƙin ciki da baƙin cikinsu. Duk wanda baya jin haka, to baya daga cikinsu (muminai).” [Majmu’u Fatawa]
Imam Ibn Al-jawzi (Rahimahullah) yace:
“Duk wanda baya son aikinsa (na kirki) ya tsaya ko ya yanke bayan mutuwarsa, to yayi kokari ya yaɗa ilimi.” [At-Tazkirah]
Annabi (SAW) yace:
“Duk wanda yacewa ƙaramin yaro zo ka karɓa, kuma yaron ya zo amma sai bai bashi komai ba, to ya sani yayi ƙarya.” [As-Sahihah]
Imam Ibn Al-Qayyim (Rahimahullah) yace:
“Lallai duk wanda yake lizimtar aikata zunubi to ya sani cewa zai kai lokacin da zai daina jin daɗin yin zunubin kuma (a jarrabeshi da) kasa daina aikatawa.” [Raudatul-Muhibbin]
Imam Ash-shanqiti (Rahimahullah) yace:
“Ƙarin aure (bisa tsarin ƙa’ida da cika sharuɗɗa) Shari’ah ce ta Allah da Manzonsa (SAW), kuma ba kowa yake sukarsa ba face wanda Allah ya makantar da basirarsa da duhun kafirci (shirka ko son Rai).” [Adwa’ul Bayan]
Imam Az-Zahabiy (Rahimahullah) yace:
“Mafi ilimin fiƙihu a cikin matayen Al’ummar nan baki ɗaya itace A’isha (RA).” [Siyaru A’lamin-Nubala]
Annabi (SAW) yace:
“Duk wanda ya Sallaci Sallar asubahi (a jam’i), to yana ƙarƙashin (kiyayewar) kulawar Allah.” [Sahihu Muslim]
Annabi (SAW) yace:
“Duk wanda ya ganni a mafarki (tare da cika sharuɗɗa), to da sannu zai ganni a farke (a lahira) domin shaiɗan baya ɗaukan kamannina (cikakkun na asali).” [Bukhari]
Imam Ibn Taimiyyah (Rahimahullah) yace:
“Dukkan wanda ya saɓa wa Manzo (SAW), to tanaƙudin sa (harmagagarsa) na kasancewa ne gwargwadon saɓawarsa.” [Bayani Talbisul Jahamiyyah]
Ibn Umar (RA) yace:
“Taƙawa ita ce kada ka kalli kanka a matsayin kafi waninka (daraja da falala a wurin Allah).” [Tafsirul Baghawi]
Imam Mutarraf Bin Abdullah (Rahimahullah) yace:
“Duk wanda yake son sanin matsayinsa a wurin Allah, to ya kalli matsayin Allah a wurinsa.” [Ahmad a cikin Zuhud]
Imam Ibn Al-Qayyim (Rahimahullah) yace:
“Yana daga alamar taɓewa; mantawa da aibin kai, da kutsawa cikin aibin wani.” [Miftahu Daris-Sa’adah]
Imam Wahab Bin Munabbih (Rahimahullah) yace:
“Idan kaji mutum yana yabon ka da abinda baka yi ba, to kada ka amintu da cewa ba zai iya zargin ka da abinda baka yi ba.” [Siyaru A’lamin-Nubalah]
Imam Ibn Qayyim (Rahimahullah) yace:
“Sallar Asubahi ita ce tushe kuma ginshiƙin ayyuka, kuma ita ce farkon sa.” [Zadul Ma’ad]
Annabi (SAW) yace:
“Mafificiyar Sallah a wurin Allah ita ce Sallar asubahi, yinin juma’ah, a cikin jam’i.” [Sahihul Jami’u]
Sheikh Bin Baz (Rahimahullah) yace:
“Wankan juma’ah na Sunnah baya tabbatuwa sai bayan fitowar Alfijir.” [Majmu’u Fatawa]
Imam Ibn Uthaimin (Rahimahullah) yace:
“Lokacin wankan Juma’ah shine bayan fitowar Alfijir ko bayan hudowar rana (yafi) ko lokacin tafiya masallaci (mafifici).” [Liqa Bab Al-maftuh]
Sheikh Ibn Uthaimin (Rahimahullah) yace:
“Duk wanda bai yi wankan juma’ah ba ya aikata saɓon Allah, saboda Annabi (SAW) yace wajibi ne akan kowane baligi.” [Alliqah Ash-Shahri]
Annabi (SAW) yace:
“Duk wanda yayi wankan juma’ah zai kasance a cikin tsarki (daga laifukansa) har zuwa wata juma’ar.” [Sahihul Jami’u]
Shaqiq (Rahimahullah) ya kasance yana umurtar iyalan gidansa maza da mata (masu niyyar fita Sallar juma’ah) da yin wankan juma’ah.” [Almusannaf]
“Jinkirin zuwa juma’ah yana sabbaba jinkirin shiga Aljannah (koda kuwa mutum yana daga ma’abotan Aljannar).” [Sahihul Jami’u]
Anas Bin Malik (Rahimahullah) yace:
“Mun kasance muna sammakon zuwa Sallar juma’ah, kuma muna yin (bacci) ƙailula bayan Sallar juma’ah.” [Sahihul Bukhari]
Annabi (SAW) yace:
“Duk wanda yayi sammakon zuwa masallacin juma’ah a sa’a ta daya yana da ladar yin sadaka da rakumi. a sa’a ta biyu yana da ladar yin sadaka da Saniya. a sa’a ta uku yana da ladar yin sadaka da rago. a sa’a ta hudu yana da ladar yin sadaka da kaza. A sa’a ta biyar yana da ladar yin sadaka da kwai.” [Bukhari da Muslim]
Ibn Uthaimin (Rahimahullah) yace:
“Yawan tsawaita huɗubah (ranar Juma’ah) yana sanya mutane gajiya da kyamatar wa’azi.” [Nurun Alad-Darb]
Annabi (SAW) yace:
“A ranar Juma’ah mala’iku suna tsayawa a ƙofofin masallaci, suna rubuta masu shigowa, idan liman ya iso sai su naɗe takardun su saurari huɗubar liman.” [Sahihul Bukhari]
Annabi (SAW) yace:
“Yana daga Sunnah, fuskantar liman (wato kallonsa) yayin huɗuɓah ranar juma’ah.” [As-Sahihah]
“Amsa sallama da amsawa mai atishawa baya inganta a yayin da limami yake hudubar juma’ah.” [Fatawa Lajnatid-Da’imah]
“Ya tabbata a Shari’ah, cewa ana yin Sallar nafilah raka’ah biyu bayan juma’ah.” [Bukhari da Muslim], “ko raka’ah hudu.” [Muslim]
Imam Ibn Al-Qayyim (Rahimahullah) yace:
“Mai niyyar yin nafilarsa ta bayan jumu’ah a masallaci zai yi raka’ah hudu ne (biyu sau biyu), idan kuma a gida ne sai yayi raka’ah biyu.” [Zadul Ma’ad]
Imam Ibn Rajab Al-hambali (Rahimahullah) yace:
“Kamar yadda Sallar dare ta ke zama sanadiyyar kankarar zunubban bawa, haka ta ke sanya ɗaukakar darajar sa.” [Lada’iful Ma’arif]
Imam Fudail Bin Iyad (Rahimahullah) yace:
“Zama a majalisin ilimi ta hanyar tausayawa da kyautata mu’amala yafi Sallar dare da azumin yini.” [Wafayatul A’yan]
Annabi (SAW) yace:
“Kada (ka sake) ka tuhumi Allah akan abinda ya zartar na ƙaddara a kan ka.” [As-Sahihah]
Imam Ubaid Bin Umair (Rahimahullah) yace:
“Ba rashin haƙuri ne zubar da hawaye ko nuna damuwa a zuciya ba, rashin haƙuri shine munana lafazi da munana zato ga Allah.” [Uddatus-Sabirin]
Umar (RA) yace:
“Babu alkhairin da Allah yayi wa mutum bayan Musulunci sama da samun ɗan’uwa (ko aboki) na kirki.” [Qutul-Qulub]
Sheikh Bin Baz (Rahimahullah) yace:
“Ana lissafa wadanda suka mutu a hatsarin mota a matsayin shahidai, saboda mutuwarsu tana kama da waɗanda gini ya ruguzo masu.” [Nurun Alad-Darb]
Sheikh Ibn Uthaimin (Rahimahullah) yace:
“Yanayin tunanin mutum yana da tasiri sosai a kan sa (Kamar yadda baban mu, marigayi Alhaji Bashir Tofah, Allah ya gafarta masa, ya sanya wa wani littafinsa suna: tunaninka kamanninka), mutum na iya tunanin rashin lafiya alhali lafiyarsa kalau kuma rashin lafiya ya kama shi. Ko kuma mutum yayi tunanin lafiyarsa kalau alhali baya da lafiya, kuma rashin lafiyar ta tafi daga gare shi, ya samu sauki.” [Alqaulul-Mufid]
Sheikh Ibn Uthaimin (Rahimahullah) yace:
“Ba ya halatta ga mace (wadda sabubba da dalilai da hujjojin aurenta suka cika) ta hana kanta ko a hana ta yin aure, akan dalili ko hujjar sai ta kammala karatun jami’ah.” [Alliqah Ash-Shahri]
Ibn Mas’ud (RA) yace:
“Ado da mace take yi iri biyu ne, na fili (da kowa ke iya ganinta dashi, tufafin ta) da na ɓoye (ga mijinta kaɗai).” [Musannaf]
Ibn Mas’ud (RA) yace:
“Yana daga adon mace na ɓoye da ya keɓanci mijinta, idanun da suka sha ado/kwalli (ko leɓɓa masu janbaki), hannu mai ado da warwaro da zobe.” [Musannaf]
Imam An-Nawawi (Rahimahullah) yace:
“Makaruhi ne tsinke gashin furfura (daga kai ko gemu).”
Imam Muqbil (Rahimahullah) yace:
“Idan liman yana cikin khuɗubar juma’ah, sai alwalarsa ta warware, to zai cigaba da khudubah har sai ya gama; mamu su jira shi, ya sake alwala don yayi masu Sallah.”
Huzaifah Bin Qatadah (Rahimahullah) yace:
“Idan kayi wa Allah ɗa’a (biyayya) a sirri (wato a ɓoye), to Allah zai shiryar da zuciyarka, ko kaƙi ko kaso.” [Sifatu-Safwah]
Imam Sufyanuth-Thawri (Rahimahullah) yace:
“Lallai ne akan mutum ya tilasta wa ɗansa yin ilimi (na addini), saboda shi (uban) abin tambaya ne akan hakan gobe Alkiyamah.” [Siyaru A’lamin-Nubalah]
Imam Ibn Al-Qayyim (Rahimahullah) yace:
“Idan zuciya ta samu haske (na imani), to tawagar alkhairi na bibiyarsa daga kowace nahiya.” [Jawabul-Kafi)
Sheikh Nasirudin Al-Albani (Rahimahullah) yace:
“Aske gemu haramun ne, wannan kuwa da ittifaƙin mazhabobi guda huɗu (shahararru).” [Mutafarrighatush Sharid]
Imam Ibn Al-Qayyim (Rahimahullah) yace:
“Ita godiya (kamar sojan kariya ne) na ni’imah, daga dukkan abinda zai sabbaba gushewarta.” [Bada’iul Fawa’id]
Imam Mujahid Bin Jabr (Rahimahullah) yace:
“Kame gani daga abubuwan haramun suna sabbaba ƙaunar Allah (kishiyar hakan kuma yana sabbaba ƙiyayyarsa).”
Sheikh Ibn Uthaimin (Rahimahullah) yace:
“Sallah ita ce sanyin idon mumini, kuma guzurinsa na (kowane) yini don haɗuwa da ubangijinsa.” [Makarimil Akhlaq]
Annabi (SAW) yace:
“Littafin Allah (AlKur’ani) shine igiyar Allah da aka zuro daga sama zuwa doron ƙasa.” [Sahihul Jami’u]
Sheikh Al-Allamatus-si’idi (Rahimahullah) yace:
“Yana daga (abubuwa) mafi kuɓutarwa daga azabar wuta, kyautatawa halittun Allah da dukiya da kuma zance.”
Imam Fudail Bin iyad (Rahimahullah) yace:
“Ina tausayawa mutane uku: 1. Mai mulkin da ya ƙasƙanta; 2. Mai arziƙin da ya talauce; 3. Malamin da duniya ke wasa da shi.” [Siyaru A’lamin-Nubalah]
Wassalamu Alaikum,
Daga Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, Okene, Jihar Kogi ~ 08038289761.
Discussion about this post