Wai shin mai ya saka ‘Yan Nijeriya, musamman ma mutanen Arewa basa iya karatu da kananan baki, sai an zana musu da manyan baki?
Mutanen mu na arewa, har a kullum sun maida kansu koma baya, kuma sun zamanto wanda basa amfani da akasarin ilimin su da wayewar su, wajen fuskantar zahirin rayuwa ta wannan zamani.
Allah (SWT) da ya hallici Dan Adam, ya sanar da shi abu mai kyau da abu marar kyau, Allah ya bawa Dan Adam tunani da hankali domin ya banbanta da Dabba, har ma Allah yace Dan Adam khalifan Sa ne a bayan kasa.
Duk da dinbin baiwar nan da Allah yayi mana, mutanen arewa bama amfani da ilimin mu da taunanin mu, wajen hange da nazarin abin da kan iya afkuwa a gaba, sannan bama nazarin zamantakewar wannan zamani, saboda karancin wayewar mu da kin yarda da junan mu, da nuna wayon rashin wayo.
Shin wane irin bacci muke yi ne, kullun muke komawa a baya a duk wani tsari da yazo, wanda kuma ita duniya gaba ta keyi ba baya ba, musamman a wannan zamani wanda in kasa ke a ka wuce ka da tako uku, to amma fintinkau na har abada.
Gangancin mutanen arewa ne, ya sanya har yanzu a akwai tazara ta a kalla shekaru 100 tsakin mu da takwarorin mu na kudu a fuskar ilimi na zamani, wannan ya sanya suke koma baya a harkar ilimi, da kuma karfin talauci.
Abin takaicin a wannan karnin na 21, har yanzu mutanen Arewa sun yarda su haifi yara su kaisu birane da kauyuka suna gararamba da yawan bara, wai da sunan neman ilimi.
Mutanen Arewa ne fa a baya a kace za a gina musu kwata (ma yankar dabbobi) suna yanka wa da sarrafa dabbobin su don kaiwa kudancin kasar nan, domin gudun asara da samun riba, amma suka yi tutsu da su da malaman su, da yan siyasar su, wai kawai don an jahilci abin da sunan addini. Sai gashi a yau za a kai dabba kudu a sayar da naman a dawo wa da mutanen Arewa kitsen, su kuma su saya suyi miya.
A yanzu ma, koda tsitsiwar da ake yi a kan chanja tsofin kudade da sabbi, ana yin ta ne a arewacin Nijeriya, domin mutanen arewa da shugabannin su sun zama koma baya wajen rungumar tasarrufi kudi na zamani, wato cashless policy, sun zamo koma baya wajen damawa da su a mu’amalar kudi, wato financial inclusion. Duk da kasancewar mutumin Arewa, tsohon gwamnan babban Bankin Kasar nan ne, ya bullo da wannan tsarin.
Wannan ya sanya jaha daya a kudanci Nijeriya take da yawan bankunan da babu su a kaf arewacin kasar nan,a yau sama da kaso 70% na kananan hukumomin kasar nan basu da bankuna. Wannan shi ya sanya tattalin arzikin kudancin Nijeriya yayiwa na Arewa fintinkau, duk da dimbin yawan al’umar su.
Maganar shugaba Buhari da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin Emafeile na cewa kwanaki 100 da aka bada domin mayar da tsofin kudade bankuna ya isa ga duk wani dan Nijeriya da ya maida kudin sa banki.
Ya kamata mu fahimta cewa, ba kawai an canja fasalin kudi bane da su maye kudaden da suke hannun mutane ba, akwai dalilai masu yawa da yasanya gwamnati yin wannan chanjin.
A Arewa yau abin takaici ne, a ce a kwana 100 mun gagara yin abin da ya kamata wajen chanja tsofin kudaden mu, ko mu sanya su a bankuna. Shin wai mutane suna tunani ne lokaci bai wuce ba na boye kudade a randuna, masakai da kuma bisnewa a kasa, har gara ta na cinye wa?
Baban gangancin mutanen arewa ma shine na imanin cewa, ai duk wani tsari da gwmnati ta zo da shi, in har ya sabawa tunanin su da fahimtar su, sai su yanke hukuncin ba zai iyu ba, ko kuma dole sai kara lokaci, domin kawai anan ganin, ai siyasa ce, kuma surutan mutane zai sanya dole gwmanati ta chanja tunani.
Amma an manta da cewa, shugabannin ba kawai kiwon mutane suke ba, har ma da kiwon tunanin su, saboda haka kullum masu mulki suna nazarin magance irin wannan tunani na mutane, saboda wannan tunanin ya kan kawo tasgaroa tsare-tsaren gwamnati.
Hakin gwmnati ne ta yi duk abu mai iyuwa wajen kare yan kasarta da ga shiga hadari, musamman na karayar tattalin arziki da kuma kare su da ga shiga haddura wanda ya jibinci jibge kudade a gida, domin shi kansa rashin zagayawar kudi a hannun al’ummah ba karamin tasgaro yake yiwa tsarin tattalin arziki ba, sannan yana yada wanzuwar talauci a tsakanin al’ummah.
A zamanin yau, ya zama dole duk wani dan kasuwa ko mai yin mu’amalar kudi da mutane ya yi hulda da banki, ya kasance yana da asusun ajiya na banki, kin yin haka, ba abin da zai haifar sai da na sani. Kin yin haka tamkar mutum ne yace a yau ba zai yi amfani da wayar sadarwa ba ta GSM.
A yau fa, ba wai daidaikun mutane ba, duk bankunan da suka ki rungumar cigaban fasahar zamani a kan harkokin mu’amalar su, sune koma baya a harkar banki, duk dan kasuwar da yake koma baya a huldar tasarfin kudade na zamani shine koma baya a wannan zamani.
Saboda haka, Shugaba Buahari da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya a kan kadda a tsawaita wannan lokacin, domin irin wannan darasin ne zai taimaki mutane nan mu, wajen rungumar al’amuran da zamani ya zo da su. Yin hakan zai chanja mummnan tunani da mutane suke yi akan biyayya da umarnin gwamnati.
Duk da kasancewar a wannan karon, akwai karancin wayar da kan al’ummah akan muhimamancin wannan chanja kudi, da kuma tsare tsaren da ya kamata abi wajen mayar da kudi bankuna. Wannan wayar da kan al’ummah bai je ga karkara ba, a da akan gayyaci ma mawaka suyi wakoki a na sanya su a gidajen redio da talabijin don fadakar da al’ummah da wayar musu da kai, a wannan karon abin yayi karanci.
A yau a kwai kalubale akan duk wasu wakilan al’ummah musamman na arewacin Nijeriya a kan wane tsari suke dashi na ilimantarwa da wayar da kai ga mutanensu, wanda ya shafi gina tattalin arizikin dai-daikun al’ummah da kuma yakar talauchi ga mutanen su? Shin wane tsari suke da shin a wajen wayar wa da mutanen su kai domin a dama da su a kan sha’anin kasa?
Ahmed Ilallah (alhajilallah@gmail.com; +234 802 595 1609)