Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya kara wa’adin kwanaki 10 ƴan Najeriya su garzaya su canja tsoffin takardun kuɗin su zuwa sabbi.
Hakan ya biyo bayan ganawar da gwamna Emefiele ya yi ne da shugaban Muhammadu Buhari a Daura.
Emefiele ya ce ” Bayan ganawa da na yi da shugaba Buhari, ya umarce ni in sanar da karin kwanaki 10 domin waɗanda ba su samu damar canja tsoffin takardun kuɗin su su canja, musamman mutanen karkara da masu sana’ar yau da kullum.
Sabbin Takardun Naira: Ina sane da matsin da talakawa suka shiga – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Asabar ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa ‘yan Najeriya ba za su fuskanci ruɗani ko matsala ba a harkokin kasuwancin su da al’amurorin su na yau da kullum.
Buhari ya ce ” Ina sane da matsalolin da mutane ke ciki a sanadiyyar canjin sabbin takardun kudi da kowa ke kokuwar samu.
” Mutanen mu musamman na karkara, suna ajiye kuɗaɗen su a gida ne domin harkokin yau da kullum. Sai dai kuma abinda nake so in sanar musu shine ana sane da su kuma gwamnati za ta shiga al’amarin ba za a bar su hannu rabbana ba.
A cikin sanarwar da Garba Shehu ya saka wa hannu, Buhari ya ce wannan tsari da aka yi na sauya fasalin takardun kuɗi an yi shi ne domin wadanda suke satar kuɗi su jibge a gidadjen su, sannan da kuma masu ƙarbar maƙusan kuɗi a hannu mutane kuɗin fansa.
A karshe ya ce a kwai wasu tsare-tsare da babban bankin kasa da sauran bankuna suka kirkiro domin ganin an warware waɗannan matsaloli cikin gaggawa.
Har zuwa wayewar ranar Asabar, mutanen Najeriya na ci gaba da kokawa da rashin sabbin kuɗi a hannun su.
Mutane na bin layika masu tsawo a bankuna domin samun takardun kudin. Sannan kuma a kasuwanni da yawa daga cikin ƴan kasuwa ba su karbar tsohon kuɗin.
Ranar 31 ga Janairu ne ranar karshe da za a iya am fani da tsoffin takardun kudin. Da ga 1 ga wata za su zama kamar yayi ne ba su da amfani.
Discussion about this post