Ɗan takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara a ranar Alhamis da safe.
Tinubu ya kai ziyarar ce kwana ɗaya bayan Buhari ya fito a bakin Kakakin Yaɗa Labaran sa, Garba Shehu ya ce ya na goyon bayan takarar Tinubu 100 bisa 100, amma ba zai saki ayyukan ofis da ke gaban sa ba, ya tafi ya na kararainar taya Tinubu ɗin kamfen jiha-jiha.
A ranar Laraba dai ce Fadar Shugaban Ƙasa ta faɗi dalilin da ya sa Buhari bai fara taya Tinubu kamfen ba.
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana dalilan da su ka hana Shugaba Muhammadu Buhari fara taya ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu kamfen ɗin takarar zaɓen, bayan fara kara-kainar kamfen tuni a faɗin ƙasar nan.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa, Garba Shehu ya sa wa hannu, ya ce Buhari na nan a matsayin sa na mai goyon bayan takarar Bola Tinubu, “amma bai bari karakainar kamfen ta ɗauke masa hankali daga ayyukan sa na Shugaban Ƙasa ba.”
A ranar Laraba ce Garba Shehu ya fitar da wannan sanarwar a matsayin amsa “domin warware damuwar da wasu ke yi ganin har yau tun da aka fara kamfen Buhari bai je ya taya Tinubu ba, duk kuwa da ya ke Buhari ɗin ne Babban Kwamandan Rundunar Yaƙin Tinubu 2023.”
Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar wa ɗaukacin ‘yan APC cewa a shirye ya ke ya yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa da sauran ‘yan takara kamfen iyakar ƙarfin sa da kishin sa.” Haka Garba Shehu ya bayyana.
Shehu ya ƙara da cewa, “yayin da Shugaba Buhari ya ke bada himma wajen ayyukan jam’iyya, to kuma akwai ayyukan shugabancin ƙasa a gaban sa, waɗanda tilas sai ya zauna ya fuskance su.”
Da yawan ‘yan Najeriya musamman ‘yan APC na tambayar dalilin da ya sa ba a ganin Buhari a wuraren kamfen ɗin TInubu.
Sanarwar Shehu na nuni da cewa zai yi wahala Buhari ya riƙa fita ya na taya Tinubu kamfen, duk kuwa da cewa shi ne Shugaban Kamfen ɗin Shugaban Ƙasa na Takarar Tinubu.
Yayin da Tinubu ke ci gaba da kamfen, Buhari ya halarci taruka da dama a ciki da wajen Najeriya, har ma da na baya-bayan nan, wanda ya je Amurka ya halarci taron Amurka da Shugabannin Afrika, wanda aka yi a Washington.
Garba Shehu ya ce ko a taron Amurka da Buhari ya halarta, sai da ya nuna goyon bayan sa ga takarar shugabancin ƙasa da Bola Tinubu ke yi a zaɓen 2023, a ƙarƙashin APC.
Discussion about this post