Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu matasa su 19 da suka halarci taron daurin auren wasu maza biyu, Abba da Mujahid a jihar.
Ranar Talata kakakin hukumar Lawan Ibrahim ya bayyana cewa Hisbah ta kama wadannan matasa ne bayan sun halarci daurin auren Abba da Mujahid wasu masoya biyu.
“Hisbah ta samu labarin wannan ɗaurin aure da aka shirya yin sa a ta bakin wani mai kishi da ya zo ya kawo karar su hukunar.
“Ma’aikatan mu dake Sharada a cikin garin Kano suka yi gaggawar dira wurin da za a ɗaura auren kuma Allah ya sa sun isa ba a ɗaura auren ba.
“A lokacin da jami’an Hisba suka dira wurin ɗaura auren basu iske ango da amarya ba wato Abba da Mujahid sun arce kafin Hisbah ta isa wurin sai dai an cafke wata mata mai suna Salma Usman wacce ita ce ta shirya wannan ɗaurin aure.
Ibrahim ya ce hukumar za ta damka wadannan mutanen da aka kama a wurin ɗaurin airen wa to waɗanda suka halarci taron ga hukumar ‘yan sanda domin aci ga a da yin bincike a kai.
Hukumar za ta ci gaba da farautar Abba da Mujahid wato ango da amaryar har sai annkama su domin a hukunta su bisa wannan kazamin aiki da suka so su aikata.