Wasu ‘yan bindigar da har yanzu ba a tantance su wa ba ne, sun yi wa masallata luguden wuta, lokacin Sallar Asubahi, a garin Ughelli, cikin Jihar Delta.
Lamarin ya faru da jijjifin safiya, inda rahotanni su ka tabbatar da an ji wa mutum 11 raunuka a cikin masallacin.
An kai harin ne a Babban Masallacin da ke kan titin Okorola. Harbe-harben ya gigita masu maƙautaka da masallacin da kuma masallata, waɗanda tsoro ya hana kowa fitowa.
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Delta, Bright Edafe, ya tabbatar da cewa an raunata mutum 11 a harin.
Waɗanda ke maƙautaka da masallacin kuma sun tabbatar da cewa maharan sun arce da mutum uku, waɗanda su ka kama a cikin masallacin.
Jakadiyar Birtaniya a Najeriya, Catriona Laing, ta bayyana harin da cewa ta’addanci ne ƙarara, kuma ta yi tir da masu irin wannan hare-haren.
Jihar Delta dai can ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP, Ifeanyi Okowa ke gwamna.
Har yanzu dai Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ba ta bada labarin kama kowa ba.
Discussion about this post