Kowa dai ya san a harkar soyyaya tsakanin mace da Namiji, yakan zama kamar gasa ne. Ko dai ace mace ta rika yin wasu abubuwa domin burge miji ko saurayi ko kuma shi namijin ya rika kai komo don ya burge matarsa ko budurwarsa.
Duk ana yin haka ne domin a zauna lafiya da kara samun soyayyar juna da kuma ganin rayuwa ya inganta a tsakanin masoyan.
A dalilin haka ne PREMIUM TIMES HAUSA ta yi muku nazari mai zurfi domin zakulo wasu abubuwa muhimmai guda 4 da idan mace ta dage a kan su za ta tafi da imanin miji ko saurayin ta ba tare da an yi tunanin afkawa cikin saɓon Allah ba ta hanyar garzayawa wurin bokaye da matsafa da a karshe sai dai ma a wulakanta, a yi da na sani.
Wadannan hanyoyin sun hada da;
1 – Yi wa miji ko Saurayi kautar nazata
Yi wa namiji kauta ta ko wacce iri ta bazata hanya ce da ke kara dankon soyayya a tsakanin masoya. Zai rika yawan yin alfahari da ke sannan kuma za ki zama abin muradin sa a koda yaushe.
2. Rangaɗa kwalliya domin burge miji ko saurayi
Kwaliya na daga cikin hanyoyin dake karkato da hankalin namiji zuwa ga mace da ko da baya son ta zai fara son ta saboda kwaliyar da take yi musamman idannya gane ana yi domin sa ne shi.
3. Mace ta samu tarbiya tun daga gida
Mace mai ɗaya gwal ce, ɗa’ar kawai kan sa na miji ya ji duk duniya babu irinta. Ta kasance mai hakuri da biyayya, namiji komai azancinsa sai ta mamaye zuciyar sa. Tarbiyya da addini na da mahimmanci ga ƴa’ mace a kogin soyayya, a waje ko a gidan aure.
4. Ta iya harka da miji a lokacin Jima’a
Duk inda aka ce mace ta iya yadda za ta kwantar wa mijin rai, ta iya ba shi dama irin yadda yake so a wurin saduwa toh lallai shi kawai zai iya sa ta mamaye mijinta, sai yadda ta yi da shi. Saboda haka mata a rike wuta.
Discussion about this post