A cigaba da ayyukan cigaba da taimako da sanatan dake wakiltar Kaduna ta tsakiya, kuma ɗan takarar gwamnan jihar Sanata Uba Sani ya ke yi, ranar Asabar ya yi wa ɗaliban jihar Kaduna dake manyan makarantun jihar tallafin kuɗin makaranta.
Sanata Uba Sani ya ziyarci ɗakin karatu da Taro na jami’ar Jihar Kaduna KASU, inda a nan ne ya raba wa ɗalibai sama da 100 tallafin kuɗin makaranta.
Sanatan ya ce ya yi wannan yunkurine saboda tallafawa ƴaƴan talakawa su iya biyan kuɗin makaranta.
Ɗaliban da suka amfana da tallafin sun haɗa da ɗalibai daga Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), Kwalejin Ilimi, Kafanchan, Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) Zariya da Nuhu Bamalli Polytechnic, Zariya.
Na ba da wannan gudummawa na tallafin kudi don samar da dama ga dimbin daliban jihar Kaduna da ba za su iya biyan kudin makaranta ba.
A ciki kawabin sa, sanata Uba ya nanata muhimmancin ilimi a matsayin abu ɗaya tilo da za mu bai wa ’ya’yan marasa galihu yin gogayya da na masu hannu da shuni. Ilimi shine mafi girman matakin.
Sanata Uba, ya kara da cewa irin wannan tallafi ba zai tsaya a nan ba, zai cigaba har bayan ya zama gwamnan jihar Kaduna.
Wani ɗalibi da ya tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA, wanda shima ya amfana da wannan tallafi na sanatan ya ce ” A na wa ganin idan da Kaduna za ta samu irin Sanata Uba 10, da ɗan takaka ya more a jihar. Da yawa daga cikin mu ba mu da kuɗin biyan kuɗin makaranta, amma yanzu sanata Uba ya share mana hawaye.
Discussion about this post