Kotun Grade A dake Karu a Abuja ta daure wami mai suna Mohammed Waziri a kurkuku bayan ta kama shi da laifin satar buhun dankalin Hausa har na naira 20,000.
Rundunar ‘yan sandan Abuja ta kama Waziri da laifin sata da ta’ammali da ganyen wiwi.
Alkalin kotun Umar Mayana ya yanke hukuncin daure Waziri a kurkuku duk da cewa ya musanta aikata laifufukan da ake zarginsa da su.
Mayana ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 15 ga Faburairu.
Lauyan da ya shigar da karar Olanrewaju Osho ya bayyana wa kotun cewa wani Samaila Haruna ne ya kawo kara ofishin ‘yan sanda dake Karu bayan Waziri ya tsallaka cikin gidan sa ya sace masa dankali.
Osho ya ce bisa ga karar da Samaila ya kawo caji ofis ya ce Waziri ya saci dankalin ne ranar 16 ga Disamba wanda kuma aka yi masa kudi zai kai naira 20,000.
Lauyan ya ce a hannun jami’an tsaro Waziri ya shaida wa ‘yan sandan cewa lalle shi ne ya saci dankalin.
Ya Kuma ce jami’an ‘yan sandan sun kama Waziri da rodi wanda bincike ya nuna cewa na Wani soja ne mai suna Peter sannan da ganyen wiwi.
Yanzu dai kotu ta tsare shi sai ta kammala bincike, an kuma yanke masa hukunci.
Discussion about this post