Mintuna 30 kafin Buhari ya isa garin Okene wurin kaddamar da katafaren asibiti da gwamnatin jihar ta gina, bom ya fashe a kusa da asibitin da ke dab da fadar sarkin Okene, Ado Ibrahim.
Akalla mutum hudu ne suka rasu sanadiyyar wannan hari da aka akai. Sai dai kuma duk da fashewar bom din bai hana shugaban Shugaban Buhari kin halartar wannan biki na kaddamar da asibitin ba.
Jami’an tsaro sun dira garin Okene, sun katange wurin da tsaro a lokacin da Buhari ya isa garin wurin kaddamar da asibitin.
Sai dai kuma Ohinoyi na Okene bai samu damar halartar taron ba saboda abinda ya faru.
Akalla mutum 4 ne suka rasu a harin da har yanzu ba a san wadanda suka kaishi ba.
Discussion about this post