Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kama wani basarake a Zaria da ya yi wa dan shekara 14 fyade.
Kakakin rundunar Muhammadu Jalige wanda shine ya sanar da haka ranar Laraba ya ce rundunar za a maka basaraken a kotu da zarar ƴan sanda sun kammala bincike akai.
Da ya ke tattaunawa da kamfanin Dillanci Labaran Najeriya wani ɗan uwan wannan yaro, Hamza Zubairu ya ce basaraken ya lalata da kanensa ne ranar 9 ga Disamba a unguwar Kwarbai.
Zubairu ya ce basaraken makwabcin su ne kuma kowa a unguwan na yi masa ganin dattijon arziki, ana daraja shi matuka.
Ya ce a wannan rana basaraken ya aiki yaron cikin dakinsa ya je ya dauko masa kudi kafin yaron ya ankare basaraken ya shigo dakin ya kulle kofar sannan ya zaro sharbebiyar takobi ya nuna wa yaron.
Zubairu ya ce basaraken ya ce zai yanka yaron idan ya yi motsi ko ya yi ihu saboda abin da zai yi masa.
Ya ce da yaron ya fito sai ya ji tsoron fadin abin da ya faru sai bayan kwanaki sai ya faɗi wa wata goggon sa.
“ Bayan goggon yaron ta saurare shi sai ta kai ƙara ofishin ƴan sandan Zariya.
Kodinatan cibiyar kula da wadanda aka yi wa fyade ‘Salama Sexual Assault Referral Center’ dake babban asibitin Gambo Sawaba a Zaria Aisha Ahmed ta ce cibiyar ta gudanar da gwaje gwaje za ta mika wa ƴan sanda sakamakon gwajin nan ba da daɗewa ba.
Discussion about this post