Shugaba Muhammadu Buhari ya fito ƙarara ya kira kasashen Yamma cewa munafukai ne.
Buhari ya yi wannan kakkausan raddin a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da Taron Magance Illocin Canji Da Gurɓacewar Yanayi (COP27) a Masar.
Shugaban na Najeriya ya yi bayanin a cikin wata maƙala da ya rubuta, kuma aka buga a jaridar Washington Post ta Amurka a ranar Laraba.
Ya kira su munafukai ne saboda a cewar sa, sun kasa cika alƙawarin magancewa da hana ci gaban illolin da canjin yanayi da gurɓacewar yanayi ke haifarwa a Afrika.
Buhari ya tunatar da ƙasashen Turawan Yamma cewa sun yi alƙawarin kashe dala biliyan 100 wajen wannan gagarimin hana illar hayaƙin makamashi yi wa Afrika illa, amma har yau ba su yi komai ba.
“Da yawa daga cikin shugabannin Afrika su na jin haushin yadda ƙasashen Turawan Yamma ke yin biris da wannan gagarimar matsalar da ke addabar Afrika, wadda kuma masana’antun Turai ne ke haddasa ta.”
Ya ce duk wasu bala’o’in da ke faruwa a ƙasashe masu tasowa sanadiyyar sauyin yanayi ko gurɓacewar sa, masana’antun Turai ne ke haddasa su.
“Saboda haka idan ƙasashen Turawan Yamma za su tashi tsaye su tashi su taimaki Afrika, amma su daina shata mana yadda za mu riƙa riƙa amfanin da arzikin mu.” Inji Buhari.
An dai shirya taron COP27 a Masar, saboda ganin cewa Afirka ce matsalar canjin yanayi ta fi shafa a ‘yan shekarun nan.
An haƙƙaƙe cewa yawan fari da ƙarancin ruwan saman da ake samu a wasu ƙasashen Afrika, tsawa da cida mai ruguza gine-gine, fantsamar wutar daji, mummunar ambaliyar ruwa da girgizar ƙasa a Afrika, duk gurɓacewar yanayi ne ke haifar da su, sakamakon illolin gurɓataccen hayaƙin da masana’antun Turai ke jaddadawa.
Discussion about this post