Babbar Kotun Tarayya dake garin Jalingo jihar Taraba ta tumbuke wa sanata Emmanuel Bwacha rawanin sa na kujerar sanata da yake akai bisa dalilin canja sheka da yayi daga PDP zuwa APC.
Alkalin Kotun , Maishari’a Simon Amobeda, ya umarci Bwacha ya gaggauta yin sallama da wannan kujera.
Jam’iyyar PDP ce ta kai karar Bwacha Kotu, inda ta roke ta ta sauke sanata Bwacha daga kujerar sanata da yake akai saboda ya sauya sheka.
Kotu ta ce Bwacha na zaman PDP ne a majalisar Dattawa, sauya sheka da yayi ya ruguza wannan auratayya ta sa da kujerar sanata, saboda haka kujerar sanatan da yake akai ta haramta masa yanzu.
Idan ba a manta ba, a cikin watan jiya wata kotu ta soke takarar sanatan ɗan takarar gwamnan jihar Taraba, na Jam’iyyar APC.
Kotun da ta yanke wannan kara ta ce ba a yi sahihin zaɓeba a lokaci n zaben fidda gwani.
Discussion about this post