Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa sababin yunwa, fatara da talauci ya jefa mutum miliyan 86 cikin rayuwar ƙunci a Arewa, yayin da lamarin ya shafi mutum miliyan 47 a Kudu.
NBS ta fitar da cikakken rahoton cewa mutane miliyan 133 ne ke fama da fatara, talauci, yunwa da ƙaƙa-ni-ka-yi a Najeriya, rahoton da rabon da ta fitar da irin sa tun cikin 2010.
Ta ce kashi 91 cikin 100 na ‘yan Jihar Sokoto a cikin ƙuncin talauci da fatara su ke. Yayin da Jihar Ondo kuwa kashi 27 ne kaɗai waɗanda ke rayuwa a jigace cikin yunwa, fatara da talauci,” inji rahoton NBS.
Jihohin da su ka fi yawan masu fama da ƙuncin fatara da yunwa a cewar NBS, su ne Sokoto, Bayelsa, Jigawa, Kebbi, Gombe da Yobe. “Amma a cikin su ba zamu iya cewa ga wacce ta fi sauran muni.”
Ƙididdigar 2018/2019 dai ta nuna cewa kashi 40.1 na ‘yan Najeriya ne matalauta, amma yanzu zuwa ƙididdigar 2022, adadin ya kai kashi 63 cikin 100.
NBS wadda hukumar gwamnatin tarayya ce, ta ce adadin ‘yan Najeriya miliyan 133 ke gaganiya cikin fatara da talauci.
Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa aƙalla ‘yan Najeriya miliyan 133 ke rayuwa cikin ƙuncin rayuwa, fatara da talauci.
NBS ta fitar da wannan sakamakon ƙididdiga a ranar Alhamis. Ta ce adadin masu fama da sababin fatara da talauci ya kai kashi 63% cikin 100% na yawan ‘yan Najeriya.
NBS ta ce fiye da kashi 50 na yawan masu fama da fatara da yunwa su na girki ne busasshen kashin shanu, katako, itace da ƙirare da kuma gawayi, maimakon gas.
NBS ta ce kashi 70 cikin 100 na al’ummar Nijeriya duk a yankunan karkara su ke. Shi ya sa kashi 80 cikin 100 na masu fama fatara da talauci.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin tsadar rayuwa ya ƙara cillawa sama yayin da ake fama da hauhawar farashi da tsadar fetur da gas.
Malejin tsadar rayuwa a Najeriya ya ƙara cillawa sama zuwa kashi 21.09 cikin watan Oktoba, 2022. Wannan ke tashin gauron zabi da ya yi sau tara a jere duk wata.
Malejin na tsadar rayuwa ya ƙara yin sama ne daidai lokacin da ake fama da tsadar kayan abinci, kamar yadda Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Kasa (NBS) ta bayyana a ranar Talata.
NBS ta yi wannan bayanin a cikin rahoton ta na Jadawalin Alƙaluman Farashin Abinci da Masarufi na watan Oktoba, 2022.
NBS ta ce malejin ya ƙaru ne, domin a cikin watan Satumba, malejin ya na kashi 20.77.
Rahoton na ranar Talata da NBS ta fitar, ta ce a duk wata farashi ƙaruwa ya ke yi har tsawon watanni tara a jere.
NBS ta ce tsadar kayan abinci ya kai har kashi 23.72% a cikin Oktoba, cillawar da ya yi sama daga kashi 23.34% a cikin watan Satumba.
Rahoton ya danganta matsalar tsadar rayuwar da fetur da gas da kuma tsadar kayan masarufi da kayan abinci.
Wanann gagarimar matsala ta shafi Najeriya a daidai lokacin da ake ta fama da ibtila’in ambaliya, wanda ya yi mummunar ɓarnar mamaye garuruwa, kashe mutum 600 da ta kashe.
Discussion about this post