Wata mata ɗa ya shafe sama da shekaru 20 ta na noma, ta bayyana cewa daga cikin manyan matsalolin da manoma mata musamman a karkaka ita hana su haƙƙin cin gadon gonaki a gidajen miji da gidan iyaye da wasu ƙabilu ke yi.
Janet Adejoh, mace mai himmar nona a Jihar Neja, ta kuma shaida wa wakilin mu cewa bai kamata a riƙa bai wa mata manoma ramcen kuɗin noma ba. Saboda ba su biya.
Ta ce kamata ya yi a riƙa ba su tallafi, saboda mata su na yawan yin asara a harkokin noma da dama.
Janet wadda mamba ce ta Ƙungiyar Mata Manoma, kuma kodineta, baya ga noman da ta ke yi, ta na kuma sarrafa rogo ta yi filawar rogo, garin rogo, filawar wajen soya da sauran su.
A yanzu haka ta ja baya da daga noma, ta bi bada ƙarfi wajen sarrafa amfanin gona.
Ta nuna yadda tun da farko matsalar rashin jarin fara sana’ar noma ya kawo mata cikas.
“A yanzu na ja baya daga yin noma, saboda shekaru na sun ja da yawa. Na fi bada ƙarfi wajen sarrafa amfanin gona ina sayarwa.”
Ta yi kukan yadda ambaliya da cutar korona su ka illata mata da dama, ta hanyar durƙusar da sana’ar noman da su ke gadara da shi.
Sai dai ta ce yanzu ta na tattara sunayen waɗanda za su bai wa Ministan Harkokin Noma domin a san irin tallafin da za a yi masu.
Ta yi maganar cewa da ya ke su mata ba su samun gadon gonaki, ta ce sun dogara ne ga aron gonaki, kuma aron ma na noma-tashi.
Daga nan ta ce su na biyan kuɗin aron gona duk hekta 1 Naira 10,000.
Ta ce matsalar ‘yan bindiga da rikice-rikicen ƙabilanci na kawo masu tawaya ga noma, saboda masu yi masu noma su na biyan su a yanzu su na tsoron zuwa gona, don kada a damƙe su ko a kashe su.
Discussion about this post