A ranar Laraba ne shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabbin kudi da aka sauya musu kala a fadar gwamnati a Abuja.
A wurin kaddamarwar Buhari ya ce dalilin da ya sa amince da a sauya fasalin naira sun haɗa da domin a samu daidaituwa a hadahadar kuɗi a kasa.
Buhari ya ce ” Tun lokacin da babban gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emiefile ya sanar da ni shirin canja naira na amince kai tsaye da dalilan da ya bani.
” Doka ta ba babban bankin kasa daman sauya fasalin kasa duk shekara 5-8. Wannan ba abu bane sabo. Kuma idan ka duba za a ga mun daɗe rabon da aka sauya fasalin kuɗin Najeriya.
“Akwai bukatar a dauki matakin gaggawa wajen sanin kudaden da ke yawo a kasuwannin kasar, da kuma magance matsalar tabarbarewar kudaden Naira da karancin takardun kudi masu tsafta da kuma karuwar jabun takardun kudin Naira. A kan haka ne na ba da izini a sake fasalin takardun naira 200, 500 da 1000.
Sannan kuma shugaba Buhari ya kara da cewa, kamfanin buga kuɗi na kasa ne ya buga kuɗin, sannan kuma an saka masa dukkan tsaro da zai hana a iya buga jabun sa.
A na shi jawabin, gwamnan babban bankin Kasa, Emiefiele ya godewa shugaban Buhari bisa amincewa da al’amarin da yayi tun farko. Ya kuma ce za a sa ido wajen gani tsarin bai samu matsala ba.
Discussion about this post