A ranar Laraba ce Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da sabbin kuɗaɗen da aka sauya wa launi, waɗanda su ka haɗa da Naira 200, 500 da 1,000.
An ƙaddamar da su a Zauren Majalisar Zartaswa na Fadar Shugaban Ƙasa, kafin majalisar ta fara taron ta na mako-mako da ta kan yi duk ranar Laraba.
A wurin, Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bayyana abin da ya sha nanatawa, cewa za a sauya launin kuɗaɗen don a magance masu buga kuɗin jabu da sauran dalilan da ya sha bayarwa.
Kuma ya ce wasu dalilan sun haɗa da cewa akwai tulin kuɗaɗen da ke hannun jama’a har Naira tiriliyan 2.77 waɗanda ba a shigar da su cikin hada-hadar bankuna. Wannan matsala a cewar sa ta na haifar da cikas ga duk wasu tsare-tsaren inganta naira ko bunƙasa tattalin arziki da CBN ke son yi.
Kowa ya yi zaton duk ranar da aka fito da sabbin launin kuɗin za a ga wani launi mai ban-sha’awa, kwarjini da cika ido a jikin kuɗaɗen. Maimakon haka, sai aka ga babu wani canji komai sai launin da aka ɗan sauya wa kalar waɗanda za a daina amfani da su.
Ganin haka kusan duk wani wanda zai tofa albarkacin bakin sa dangane da sabbin takardun kuɗin, sai ya kushe su. Daga masu cewa an yi asarar buga sabbi, sai masu cewa ba ta sauya zane ba.
Tun daga ranar da aka yi sanarwar sauya launin kuɗin, kamar na sani, da wahala idan ina rubutu na rubuta za a yi canjin kuɗi. Sai dai na rubuta cewa “za a sauya launin kuɗi.” Sai ga shi kuwa ba canjin ba ne aka yi, launi ne kawai aka canja wa waɗanda za a daina amfani da su.
Jama’a na ta yi wa kuɗaɗen shegantaka, barkwanci, ba’a da gwasalewa. Ko ma dai me za a ce, to lamarin sauyin launin kuɗin nan ya yi kama da na hannun mu ne aka tara aka kai su wurin marina su ka yi masu turi, irin wanda ake sa zabibi a sauya wa farin gwado ko gyauto ko fatari launi.
Ban san dalilin da ya sa ƙungiyar marina tufafi ko masu rina shadda fara su maida ta ganila ba su kai takardun neman kwangilar ba su aikin sauya wa nairorin launi ba.
Da su aka ba aikin, wataƙila sai launin ya fi fitowa rangaɗau.
Ko naira biliyan nawa aka kashe wajen aikin turin waɗannan sabbin kuɗaɗe? Za mu jira mu ji.
Discussion about this post