Babban rashin adalci ne da har wakilin gidan talbijin na Channels TV ya kira dandazon magoya bayan da su ka taru wurin buɗe Sakateriyar NNPP a Legas wai “ɗaruruwan magoya baya.” Jaridar Vanguard da sauran jaridu sun buga cewa dubban jama’a ne su ka taru sanye da jajayen huluna, kamar yadda hotunan da aka yaɗa a soshiyal midiya su ka tabbatar.
A ranar Laraba ce ɗan takarar shugaban ƙasa a NNPP, Rabi’u Kwankwaso ya buɗe Sakateriyar NNPP a Jihar Legas. An buɗe ofishin a daidai kusa da tashar hawa motoci ta Fabeyi Bus Stop da ke Ikorodu.
Cincirindon agoya bayan Kwankwaso musamman bubban ‘yan Arewa mazauna Legas da sauran ƙabilu ne su ka yi dandazo a wurin.
Kwankwaso ya buɗe ofishin sa a Legas, daidai lokacin da APC wadda Tinubun Legas ne ɗan takarar ta ke fama da gaganiyar rikicin yadda za ta fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa.
An yi zama har sau biyu, amma har yau an kasa sanya ranar fara rangadin, tun bayan fito da sunayen baraden yaƙi su 442, sunayen da su ka janyo ce-ce-ku-ce da kuma ƙorafi daga dukkan gwamnonin APC.
Cincirindon magoya bayan da Kwankwaso ya tara a Legas wurin buɗe ofishin jam’iyya, ya ƙara tabbatar da cewa za a yi wa ƙuri’un jihar Legas ‘ayaga’ ne tsakanin jam’iyyu huɗu.
Ko shakka babu Tinubu ka iya yin rinjaye a Jihar Legas. To amma kuma ba zai ji daɗin sakamakon ba, domin ko tantama babu sai LP jam’iyyar Peter Obi, PDP da NNPP kowace ta yagi kaso mai tsoka a Legas.
Tinubu zai so ya ga ya yi wa sauran jam”iyyu ‘kayen-raba-ni-da-yaro’ a Legas. Amma kuma hakan ba zai yiwu ba idan aka yi la’akari da yadda ƙabilun Igbo mazauna Legas su ka rungumi Obi, Hausawa da Fulanin Legas su ka rungumi NNPP, sai kuma yadda wasu Kiristoci da dama su ka lashi takobin zaɓen PDP ko LP a Legas, saboda haushin yadda APC ta ɓullo da takarar Muslim-Muslim.
Irin wannan ‘ayaga’ ce za a yi a jihar Kano, inda APC na gani NNPP za ta yagi ƙuri’u masu ɗimbin yawa, yayin da PDP kuwa rigimar cikin gida na ɗan takarar gwamna da kuma ficewar Kwankwaso daga jam’iyyar ya kassara ta a jihar.
Cikin wata hira da PREMIUM TIMES Hausa ta yi a watan Agusta da dattijo kuma jigon NNPP, Buba Galadima, ya bayyana irin shirin da NNPP ta yi a faɗin ƙasar nan, domin tunkarar zaɓen shugaban ƙasa a 2023.
Lamarin da ke ci gaba da wanzuwa a yanzu ya na ƙara tabbatar da cewa NNPP fa da gaske ta ke yi, ba burga ko tayar da ƙura ta ke yi ba.
Matsalolin da PDP da APC su ka ƙyanƙyashe a cikin gidajen su ka iya zama alheri ga NNPP, musamman idan talakawa su ka kalli manyan jam’iyyun biyu da su ka mulke su cewa ba su da wani bambanci, tamkar Jummala ce da Jummalo, duk dai ranar Juma’a aka haife su.
Discussion about this post